INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN A. U. Saraki Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Hon. Musa Kambai Sumaila
An samu labarin rasuwar Hon. Musa Kambai Sumaila, tsohon Kantoman Ƙaramar Hukumar Sumaila. A sakon ta’aziyyarsa, A. U. Saraki ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, ’ya’yansa, da kuma daukacin al’ummar Ƙaramar Hukumar Sumaila bisa wannan babban rashi. Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin, Ya jiƙansa da rahama, Ya yalwata kabarinsa, Ya haskaka masa shi, tare da sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Haka kuma, ya roƙi Allah Ya ba iyalan marigayin da ’yan uwansa haƙurin jure wannan rashi. Allah Ya jikansa da rahama. Amin. — A. U. Saraki