WUNTI YA YI KIRA GA NIGERIA TA FAƊAƊA HANYOYIN SAMUN MAKAMASHI
Babban Daraktan Hukumar Majalisar Makamashi ta Duniya (World Energy Council Nigeria), Dr. Bala Maijama’a Wunti, ya sake jaddada buƙatar Najeriya ta gaggauta faɗaɗa hanyoyin samar da makamashi ta hanyar amfani da albarkatun makamashi masu sabuntawa da waɗanda ba sa sabuntawa da ƙasar ke da su.
Dr. Wunti ya bayyana cewa Najeriya tana da dimbin albarkatun makamashi da za su iya biyan buƙatun cikin gida tare da bayar da gagarumar gudummawa ga samar da makamashi a duniya.
Ya jaddada cewa akwai buƙatar ƙasar ta samar da ingantaccen tsari da zai haɗa hanyoyin makamashi daban-daban domin tabbatar da samun makamashi mai inganci, araha kuma ga dukkan 'yan Najeriya.
Ya bayyana hakan ne yayin gabatar da lacca a bainar jama'a da aka gudanar a jihar Bauchi a ranar Juma'a, ƙarƙashin shirin Wunti Al-Khayr Foundation, mai taken “Lead Where You Stand: Character, Citizenship and the Common Good.”
A cewarsa, faɗaɗa hanyoyin samar da makamashi na da matuƙar muhimmanci wajen gina fannin makamashi mai ɗorewa da juriya, wanda zai iya biyan buƙatun da ke ƙaruwa, tallafa wa harkokin tattalin arziki tare da samar da mafita mai ɗorewa ga ƙalubalen makamashi da Najeriya ke fuskanta.
Dr. Wunti ya kuma jaddada muhimmancin amfani da albarkatun makamashi na ƙasar yadda ya kamata, tare da bunƙasa kirkire-kirkire, jawo hannun jarin masu zuba jari da ƙarfafa haɗin gwiwar dabaru domin inganta kayayyakin more rayuwar makamashi da tsarin rarraba shi.
Ya ƙara da cewa samar da ingantaccen tsarin makamashi mai ɗorewa da hanyoyin samarwa daban-daban zai taimaka wajen inganta rayuwar al'umma, bunƙasa masana'antu, samar da guraben ayyukan yi, ƙarfafa tsaron ƙasa da kuma bai wa Najeriya damar taka muhimmiyar rawa a sauyin tsarin makamashi na duniya.
Insight Tribune News

Comments
Post a Comment