HON. BLDR. DR. MUHAMMAD UBA YA JAGORANCI ZAGAYEN KADDAMAR DA YAƘIN NEMAN ZAƁEN GWAMNA A BIRNIN KUDU


 


Birnin Kudu, Jigawa State | Insight Tribune News | 17 November 2026


Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu, Hon. Bldr. Dr. Muhammad Uba, ya jagoranci gagarumin zagayen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen gwamna a Birnin Kudu, ƙarƙashin jagorancin mai ɗakin Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa, Ambasada Hajiya Amina Mallam Umar Namadi Ɗanmoɗi.


Zagayen wanda ya gudana a yammacin ranar Talata, 17 ga Nuwamba, 2026, ya fara ne da misalin ƙarfe 3:30 na yamma zuwa 6:30 na yamma, inda al'umma daga sassa daban-daban na ƙaramar hukumar suka fito domin nuna goyon baya da haɗin kai.


An fara zagayen ne daga ƙofar gidan Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Mallam Bala Ibrahim MAMSA, inda aka bi ta Tsamiya, Masallacin Juma'a na Odoji, Kankarofi, har zuwa Layin Mahauta. Daga nan ne tawagar ta isa babban filin makarantar firamare ta Yakubu Pilot, inda aka gudanar da babban taron.


Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan siyasa da masu ruwa da tsaki, ciki har da Hon. Engr. Sulaiman Da'u Aliyu, mai neman kujerar wakilcin Birnin Kudu da Buji; wakiliyar mai neman kujerar Sanatan Jigawa ta Tsakiya; Hon. Sagiru Inuwa, mai neman kujerar Majalisar Dokokin Jiha, da sauran manyan baƙi.


A madadin Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu, Hon. Bldr. Dr. Muhammad Uba, ya miƙa saƙon jinjina da godiya ga al'ummar Birnin Kudu, maza da mata, bisa yadda suka fito ɗumbin jama'a domin tarbar mai ɗakin Gwamna da tawagarta.


Ya kuma yaba da yadda aka gudanar da zagayen cikin kwanciyar hankali, lumana da nuna kyakkyawar tarbiyya, ba tare da hayaniya ko tashin hankali ba.


A ƙarshe, Builder ya miƙa saƙon ban-gajiya ga mai ɗakin Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa, Ambasada Hajiya Amina Mallam Umar Namadi Ɗanmoɗi, tare da dukkan ƴan tawagarta, yana musu fatan Allah Ya sauƙaƙa musu tafiya, Ya mayar da su gidajensu lafiya.


INSIGHT TRIBUNE NEWS

Committed to Credible and Responsible Journalism.

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS

PROF. HADIZA ABDULLAHI USMAN HONOURED WITH FPA LONDON AWARD 2026 FOR EXEMPLARY LEADERSHIP IN HEALTHCARE