NNPC RETAIL ZA TA BAR RIBAR SAYAR DA MAN FETUR, TA SAYAR WA ‘YAN NAJERIYA A FARASHIN SAMUWA, YAYIN DA GWAMNATIN TARAYYA KE ƘARA ƊAUKAR MATAKAN SAUƘAƘA TASIRIN MATSALAR MAN FETUR TA DUNIYA



Kamfanin Nigerian National Petroleum Company (NNPC) ya amince a yau da barin ribar da yake samu daga sayar da man fetur, domin sayar da man ga ‘yan Najeriya a farashin da ya samo shi, a matsayin wani mataki na rage wa gidaje masu rauni tasirin tashin farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.


NNPC Retail, wanda a halin yanzu ke sayar da man fetur a ɗaya daga cikin mafi ƙarancin farashi a kasuwa, zai fara aiwatar da wannan sabon tsarin na tsawon kwanaki 30.


Wannan na nufin idan farashin saukar da man fetur na NNPC ya kai Naira 1,300 kan lita, kamfanin zai sayar wa ‘yan Najeriya, musamman masu motocin haya, a kan Naira 1,300 kan lita.


Wannan mataki na rangwame daga NNPC Retail, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi, yana daga cikin matakan da Ministan Kudi kuma Ministan da ke kula da Tattalin Arziƙi, Taiwo Oyedele, ya sanar a yau.


Oyedele ya bayyana fatan cewa sauran ‘yan kasuwar man fetur za su yi koyi da wannan mataki na NNPC, kasancewar ana sa ran tashin farashin ɗanyen mai da na man fetur ba zai daɗe ba.


Oyedele ya jaddada cewa wannan mataki na NNPC na sayar da man fetur da rangwame bai kamata a fassara shi da cewa an dawo da tallafin man fetur ba, domin an kawo ƙarshen tallafin man fetur tun ranar 29 ga Mayu, 2023.


SAYAR DA ƊANYEN MAI GA MATATUN CIKI


Bugu da ƙari, Oyedele ya sanar da shirin sayar da ɗanyen mai tun da wuri ga matatun mai na cikin gida.


Yayin da samar da ɗanyen mai ke ƙaruwa kuma aka saki ɗanyen man da aka riga aka ware wa wasu yarjejeniyoyi, ana sa ran wannan mataki zai taimaka wajen kare farashin man fetur daga sauye-sauyen farashin kasuwar duniya.


Oyedele ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya tana tattaunawa kan sanya iyakar Naira 1,350 kan kowace lita a farashin man fetur daga matatar mai ko kuma farashin saukar da man fetur, domin tabbatar da daidaiton farashin man a gidajen mai.


Idan farashin samarwa ya haura wannan iyaka, matatun mai da masu shigo da man fetur za su ɗauki gibin na ɗan lokaci, sannan su dawo da kuɗin daga baya idan farashin ɗanyen mai ko canjin kuɗi ya samu sauƙi, ba tare da karya wannan iyaka ba.


Oyedele ya ce:


«“Wannan ba tallafi ba ne, kuma ba tsarin kayyade farashi ba ne. An tsara shi ne domin daidaita farashi a tsawon lokaci maimakon danne shi.”»


Ya ƙara da cewa tsarin zai taimaka wajen rage tasirin sauye-sauyen farashi ga ‘yan Najeriya, sannan za a dinga bitar iyakar farashin a kowane wata tare da bayyana sabbin alkaluman domin tabbatar da gaskiya da rikon amana.


TAKAITAWA KAN HARAKAR HARAJI DA KUƊADEN HANYOYI


Oyedele ya kuma bayyana cewa, ƙarƙashin dokokin gyaran haraji na shekarar 2025, Gwamnatin Tarayya tare da jihohi da hukumomin tsaro za su ƙara ɗaukar matakan dakile tarin wasu haraji da kudaden hanya da ke ƙara tsadar sufuri da jigilar kayayyaki.


Gwamnatin Tarayya za ta kuma ƙara kuɗaɗen tallafin kuɗi ga gidaje mafi rauni tare da faɗaɗa rancen kuɗi mai sauƙi ga ƙananan ‘yan kasuwa da masu amfani da kayayyaki.


ƘARA SAURIN YAƊA AMFANIN CNG


Gwamnatin Tarayya tana ƙara faɗaɗa amfani da CNG tare da haɗin gwiwar gwamnatocin jihohi.


Ana sa ran masu motocin haya za su mayar da raguwar kuɗin da suke kashewa wajen amfani da CNG ga fasinjoji ta hanyar rage kuɗin sufuri.


CNG ya fi man fetur arha da kusan kashi 60 zuwa 70 cikin 100.


HARAXIN RIBA MAI YAWA


Gwamnatin Tarayya za ta yi la’akari da sanya harajin riba mai yawa ga kamfanoni ko masu gudanar da harkokin makamashi da suka yi amfani da yanayin kasuwa wajen cin moriyar masu amfani da kayayyaki fiye da kima.


Gwamnati ta ce za a yi amfani da kuɗin da aka samu daga irin wannan haraji wajen rage wa jama’a tasirin tsadar man fetur, musamman ta hanyar tallafin sufuri ko baucan ga ma’aikatan birane masu karamin albashi.


Gwamnatin Tarayya za ta kuma yi aiki tare da Majalisar Dokoki ta Ƙasa domin duba yiwuwar ƙara rangwamen haraji ga masu ƙaramin ƙarfi a ƙarƙashin Dokar Kuɗi ta 2027.


RAGE TSANGWAMA DA KUDADEN KULA DA HARKOKI


Gwamnatin Tarayya tana kuma rage wasu tsare-tsare da kudaden gudanarwa waɗanda ke ƙara tsadar gudanar da kasuwanci, wanda daga ƙarshe ke iya ƙara farashin kayayyaki da ayyuka.


KAFUWAR NATIONAL STRATEGIC FUEL RESERVE


Domin kare gidaje da ‘yan kasuwa daga irin wannan matsalar makamashi a nan gaba, Gwamnatin Tarayya za ta zuba jari wajen kafa National Strategic Fuel Reserve.


A ƙarƙashin wannan tsari, gwamnati za ta iya fitar da man da aka tace zuwa kasuwa bisa ƙa’idoji bayyanannu da aka wallafa, a duk lokacin da matsalar samar da man fetur a duniya ko boye man ta yi barazana ga wadata da daidaiton farashi.


Gwamnati ta jaddada cewa wannan ba tallafin man fetur ba ne, kuma ba wai yana kayyade farashi ba ne. Manufarsa ita ce tabbatar da wadatar man fetur da rage sauye-sauyen farashi.


Hakan zai taimaka wajen hana ƙarancin man da aka ƙirƙira, dakile magudin kasuwa da kuma ƙarfafa tsaron makamashi na dogon lokaci.


INGANTA HARKAR CUNKOSON HANYOYI DA JIGILAR KAYAYYAKI


Hukumomin kula da zirga-zirgar ababen hawa za su ƙara inganta yadda ake tafiyar da cunkoson ababen hawa, musamman a manyan birane, domin rage yawan man da ake amfani da shi.


Haka kuma, sabbin lambobin adireshi da NIPOST ta ƙaddamar za su taimaka wajen inganta harkar jigilar kayayyaki tare da rage kuɗin gudanar da ita.


GWAMNATI: BA A MAIDO DA TALLAFIN MAN FETUR BA


Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewa babu wani daga cikin waɗannan matakai da ke nufin dawo da cikakken tallafin man fetur.


Gwamnati ta ce dawo da irin wannan tallafi zai iya haifar da matsalolin dogon lokaci domin magance wata matsala ta ɗan lokaci.


Fadar Shugaban Ƙasa ta amince cewa cire tallafin man fetur ya zo da tsadar rayuwa ga ‘yan Najeriya, amma ta ce madadin tsarin tallafin da aka yi amfani da shi a baya ya haifar da matsaloli kamar ƙarancin man fetur, fitar da man zuwa ƙasashen waje ba bisa ka’ida ba, durƙushewar kuɗin ƙasa da kuma matsalar kuɗaɗen gwamnati.


Fadar Shugaban Ƙasa ta ce ba ta da niyyar mayar da tsarin da aka yi watsi da shi, amma tana son tabbatar da cewa amfanin sauye-sauyen tattalin arzikin da ake yi ya isa ga ƙarin ‘yan Najeriya cikin sauri kuma ta hanyar da za su iya gani.


Gwamnatin Tarayya ta kuma bayyana cewa tana aiki kan cikakken kunshin matakan tattalin arziki da nufin rage hauhawar farashin kayayyaki zuwa ƙasa da kashi 10 cikin 100 cikin ɗorewa a nan gaba.


Bayo Onanuga

Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman

(Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa)


8 ga Oktoba, 2026

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

Prof. Hadiza Abdullahi Usman Celebrates Prof. Ahmed Ahidjo on Inaugural Lecture and Send-Forth

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS