IOM: Mutane Sama da 874,000 na Fuskantar Barazanar Rasa Matsugunansu a Somalia
Hukumar IOM ta yi gargaɗin cewa ambaliya na iya tilasta wa dubban iyalai barin gidajensu cikin watanni uku masu zuwa.
Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM) ta yi gargaɗin cewa kimanin mutum 874,319 na iya rasa matsugunansu a Somalia tsakanin Oktoba da Disamba na shekarar 2026 sakamakon barazanar ambaliya.
Hukumar ta bayyana cewa cikar koguna da mamakon ruwan sama na ƙara barazana ga al'ummomin da tuni suke fama da matsalolin fari da kuma yawan ƙaura daga muhallansu.
Shugaban IOM a Somalia, Manuel Marques Pereira, ya ce akwai fargabar cewa dubban iyalai za su rasa gidajensu na tsawon makonni, musamman ganin cewa mutane da dama sun riga sun rasa matsugunansu, kuma ba su da isassun hanyoyin da za su iya tinkarar sabon bala'in.
Ya yi kira da a samar da tallafin kuɗi cikin gaggawa domin taimaka wa al'ummomin da ke cikin haɗari wajen kare rayukansu da dukiyoyinsu.
Wani hasashe da IOM ta fitar tare da Hukumar 'Yan Gudun Hijira ta Denmark (DRC) ya nuna cewa ambaliya ce za ta haddasa kusan kashi 92 cikin 100 na ƙaurar da ake hasashen za ta faru a wannan lokaci.
Gargaɗin na zuwa ne yayin da Somalia ke shiga lokacin damina, inda ake hasashen samun ruwan sama fiye da yadda aka saba sakamakon tasirin yanayin El Niño.
IOM ta kuma bayyana cewa zuwa yanzu ta samu kashi 14.4 cikin 100 ne kawai na kuɗaɗen da take buƙata domin gudanar da shirinta na tunkarar ambaliyar, lamarin da ke nuna ƙarancin tallafin da ake da shi domin fuskantar matsalar.
Tuni dai aka fara samun alamun ambaliya a yankunan Doolow, Jowhar da Baidoa. Haka kuma, ana hasashen cewa Beledweyne da Gaalkacyo na daga cikin wuraren da za su iya fuskantar mummunar barazanar ƙaura sakamakon ambaliyar.
Hukumar ta jaddada muhimmancin ɗaukar matakan gaggawa da samar da isasshen tallafi domin rage illar ambaliyar da kuma kare rayukan al'ummar Somalia.
Daga: Insight Tribune News
Your Trusted Source for Reliable News.

Comments
Post a Comment