DR. ADAMU ABDULLAHI ATTERWAHMIE YA YI TA'AZIYYAR RASUWAR MAHAIFIN TSOHON KAKAKIN MAJALISAR DOKOKIN JIHAR JIGAWA, RT. HON. IDRIS GARBA KAREKA
Dr. Adamu Abdullahi Atterwahmie ya mika sakon ta'aziyyarsa ga Rt. Hon. Idris Garba Kareka, tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa kuma dan majalisar da ke wakiltar Karamar Hukumar Jahun, bisa rasuwar mahaifinsa.
Labarin rasuwar mahaifin Rt. Hon. Idris Garba Kareka ya jefa iyalansa, abokan arziki da sauran makusantansa cikin alhini da jimami.
A sakon ta'aziyyarsa, Dr. Atterwahmie ya bayyana alhininsa bisa wannan babban rashi, tare da mika sakon jaje ga iyalan mamacin da addu'ar Allah Madaukakin Sarki Ya ba su hakurin jure wannan rashi.
Ya roki Allah cikin ikonsa da rahamarsa Ya gafarta wa mamacin kura-kuransa, Ya jikansa da rahama, Ya haskaka kabarinsa, sannan Ya sanya Aljannatul Firdaus ta zama makomarsa.
Haka kuma, ya yi addu'ar Allah Ya bai wa iyalan mamacin da sauran wadanda wannan rashi ya shafa juriyar wannan jarabawa, tare da tabbatar musu da cewa mutuwa kaddara ce da babu makawa ga kowane mai rai.
SAKON TA'AZIYYAR DR. ADAMU ABDULLAHI ATTERWAHMIE
“Inna Lillahi Wa Inna Ilaihir Raji'un. Ina mika sakon ta'aziyyata ga Rt. Hon. Idris Garba Kareka da daukacin iyalansa bisa wannan babban rashi. Ina rokon Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta wa mamacin, Ya jikansa da rahama, Ya sanya Aljannatul Firdaus ta zama makomarsa, sannan Ya ba iyalansa hakuri da juriya. Amin.”
A nasa bangaren, Insight Tribune News na mika sakon ta'aziyya ga Rt. Hon. Idris Garba Kareka da daukacin iyalansa bisa wannan rashi na mahaifi.
Muna rokon Allah Ya gafarta wa mamacin, Ya sanya rahama ta kasance tare da shi, Ya ba iyalansa hakurin jure wannan babban rashi.
Allah Ya jikansa da rahama. Amin, ya Rabbal Alamin.
Insight Tribune News
Majiyarku Mai Inganci Ta Labarai

Comments
Post a Comment