Builder Hon. Muh'd Uba Ya Yaba wa Gwamnan Jigawa Kan Ci Gaban Jihar, Musamman Noma da Tattalin Arziki


 Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Builder Hon. Muh'd Uba, ya yabawa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, FCA, bisa kokarin da yake yi wajen inganta rayuwar al’ummar jihar da kuma bunkasa tattalin arzikin Jigawa.


Hon. Muh'd Uba ya bayyana cewa, daga cikin abubuwan da suka fi jan hankalinsa akwai yadda gwamnatin jihar ke bai wa bangaren noma, samar da ayyukan yi da habaka tattalin arziki muhimmanci.


Ya ce irin shirye-shiryen tallafawa manoma da bunkasa noman zamani, ban ruwa, sarrafa amfanin gona da samar da kasuwannin amfanin gona na taimakawa wajen kara samar da abinci da kuma bude sabbin hanyoyin samun kudin shiga ga al’umma.


A cewarsa, noma na daga cikin ginshikan tattalin arzikin Jigawa, don haka zuba jari a wannan fanni na da matukar muhimmanci wajen samar da aikin yi, rage radadin talauci da karfafa dogaro da kai. Tsare-tsaren gwamnatin jihar na 2026–2028 ma sun sanya ci gaban noma da bunkasa kananan da matsakaitan sana’o’i cikin manyan abubuwan da za a mayar da hankali a kai.


Builder Hon. Muh'd Uba ya kuma yaba da kokarin gwamnatin jihar wajen samar da tallafi ga manoma, musamman mata da matasa, tare da karfafa tsarin noma mai amfani da fasaha da ingantattun hanyoyin samar da amfanin gona.


Ya bayyana cewa irin wadannan manufofi na da tasiri wajen bunkasa tattalin arzikin karkara da kuma samar da damammaki ga matasa.


Ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Jigawa da su ci gaba da tallafawa shirye-shiryen ci gaban jihar, tare da yin amfani da damar da ake samarwa a fannin noma da sauran bangarorin tattalin arziki.


A karshe, Hon. Muh'd Uba ya bayyana fatansa cewa kokarin gwamnatin jihar zai kara haifar da ci gaba mai dorewa, ingantaccen tattalin arziki da karin damammaki ga al’ummar Jigawa.

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

Prof. Hadiza Abdullahi Usman Celebrates Prof. Ahmed Ahidjo on Inaugural Lecture and Send-Forth

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS