ƘADDAMAR DA KUƊIN AKWATU II: SHUGABAN ƘARAMAR HUKUMAR BIRNIN KUDU YA CI GABA DA ZAGAYEN MAZAƁU, YA ZIYARCI KIYAKO DA WURNO


 


Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu, Hon. Bldr. Dr. Muhammad Uba, ya ci gaba da zagayen mazaɓu 11 da ya ƙaddamar domin ƙarfafa tsarin tafiyar da harkokin jam'iyyar APC, wayar da kan shugabannin akwatuna da sauran mambobin jam'iyyar, tare da ƙaddamar da kuɗaɗen akwatuna.


A ci gaba da wannan shiri, tawagar mai girma shugaban ƙaramar hukumar ta kai ziyara mazaɓu biyu a yau, waɗanda suka haɗa da:


1. Mazaɓar Kiyako.



2. Mazaɓar Wurno.




Tawagar ta ƙunshi manyan jiga-jigan jam'iyyar APC, da masu taimaka wa shugaban ƙaramar hukumar, ciki har da Haladu Maigari (DG), Hon. Badamasi Musa (Ministan Jinƙai), Alaramma Mallam Rabiu Sundimina, Sulaiman Range (Youths), Sunusi Ibrahim (P.A), Alh. Yusif Isah Wurno (Vice), Baba BT Wurno, da sauran al'umma tare da ƙwararrun 'yan jarida.


Saboda girman mazaɓun da kuma kasancewar ranar Juma'a, kwamitin ya takaita ziyarar yau zuwa mazaɓun biyu da aka ambata.


Wannan tsari da Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu ta fara aiwatarwa a ƙarƙashin jagorancin Hon. Bldr. Dr. Muhammad Uba, na daga cikin matakan ƙarfafa haɗin kai, wayar da kan al'umma, farfaɗo da ayyukan jam'iyyar APC da inganta hulɗa tsakanin shugabanni da mambobin jam'iyyar.


NASARORI DA SAURAREN ƘORAFE-ƘORAFE


Tun bayan fara wannan shiri, an fara samun nasarori masu ƙarfafa gwiwa, inda jama'a ke samun damar gabatar da ƙorafe-ƙorafensu da buƙatunsu kai tsaye ga shugaban ƙaramar hukumar.


Shugaban ya kasance mai sauraron koken al'umma, inda yake ƙoƙarin magance matsalolin da suka taso nan take, yayin da waɗanda ke buƙatar ƙarin tsari ko kulawa yake ɗaukar matakan tura su ga hukumomin da abin ya shafa domin samun mafita.


Wannan shiri na nuna ƙudurin shugabancin Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu na ƙarfafa tsarin shugabanci na kusa da jama'a, tare da tabbatar da cewa an saurari muradun al'umma a dukkan mazaɓu 11 na ƙaramar hukumar.


Birnin Kudu na ci gaba da tafiya bisa tsarin haɗin kai, wayar da kai da inganta shugabanci.

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS

PROF. HADIZA ABDULLAHI USMAN HONOURED WITH FPA LONDON AWARD 2026 FOR EXEMPLARY LEADERSHIP IN HEALTHCARE