WUNTI INTERNATIONAL ACADEMY: DR. BALA MAIJAMA’A WUNTI YA ƘARA ZUBA JARI A ILIMI, AL’UMMAR BAUCHI SUN YABA


 Al’ummar Wunti da ma sauran al’ummar Jihar Bauchi sun bayyana matuƙar farin ciki da jin daɗinsu kan kafa Wunti International Academy a Wunti, wani muhimmin shiri da aka samar domin ƙarfafa harkar ilimi da samar da ingantacciyar makoma ga yara da matasa.


Wannan gagarumin shiri ya sake tabbatar da hangen nesa da kishin ci gaban al’umma da Dr. Bala Maijama’a Wunti ke nunawa, musamman wajen ba da muhimmanci ga ilimi a matsayin ginshiƙin ci gaban al’umma.


Kafa makarantar a Wunti ba wai kawai samar da wurin karatu ba ne, illa dai wata babbar dama ce da za ta taimaka wajen gina ƙarni mai ilimi, tarbiyya da ƙwarewa, tare da rage wa iyaye wahalar neman ingantaccen ilimi ga ‘ya’yansu.


Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa irin wannan aiki na ɗorewa ya cancanci yabo, domin amfaninsa ba zai tsaya ga yau ba, zai ci gaba da amfani ga al’umma na shekaru masu zuwa.


Wunti International Academy na ɗaya daga cikin ayyukan da za su bar tarihi mai kyau a zukatan al’umma, musamman ganin yadda ilimi ke taka muhimmiyar rawa wajen gina al’umma mai ƙarfi da cigaba.


Muna miƙa saƙon yabo da godiya ga Dr. Bala Maijama’a Wunti bisa wannan kyakkyawan tunani da gagarumar gudummawa da ya bayar wajen ci gaban ilimi a Wunti da Jihar Bauchi.


Allah Ya saka masa da mafificin alheri, Ya ƙara masa lafiya, hikima da ikon ci gaba da ayyukan alheri domin amfanin al’umma.


✍️ Alh. Umar Umb Bauchi

Director General, Bala Wunti Focus Media

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

Prof. Hadiza Abdullahi Usman Celebrates Prof. Ahmed Ahidjo on Inaugural Lecture and Send-Forth

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS