SHUGABANCIN FMC BIRNIN KUDU YA KAI ZIYARAR TA’AZIYYA FADAR SARKIN GUMEL
Gumel, Jihar Jigawa — Asabar, 5 ga Satumba, 2026
Shugabancin Federal Medical Centre (FMC) Birnin Kudu, karkashin jagorancin Daraktan Kiwon Lafiya na Cibiyar, Dr. Adamu Abdullahi Atterwahmie, ya kai ziyarar ta’aziyya a Fadar Mai Martaban Gumel, bisa rasuwar Marigayi Sarkin Gumel.
A yayin ziyarar, Dr. Atterwahmie tare da sauran mambobin shugabancin cibiyar sun mika sakon ta’aziyyarsu ga Majalisar Masarautar Gumel, iyalan marigayin da kuma daukacin al’ummar Gumel bisa wannan babban rashi.
Dr. Atterwahmie ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ga masarautar da al’ummar Gumel, tare da addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya jikansa, Ya sa Aljannar Firdausi ce makomarsa.
Ya kuma roki Allah Ya bai wa iyalan marigayin, Majalisar Masarautar Gumel da daukacin al’ummar masarautar hakuri da juriyar wannan babban rashi.
Ziyarar ta kara nuna yadda Shugabancin FMC Birnin Kudu ke mutunta tare da kulla kyakkyawar alaka da sarakunan gargajiya da al’ummomin da take yi wa hidima.
Insight Tribune News
Gumel, Jihar Jigawa

Comments
Post a Comment