Kwairanga Ya Ce IPO na Dangote Refinery Zai Bunkasa Kasuwar Jari ta Najeriya
Group Chairman na Nigerian Exchange Group (NGX), Alhaji (Dr.) Umaru Kwairanga, ya bayyana kyakkyawan fata cewa fara sayar da hannayen jarin Dangote Petroleum Refinery ga jama’a zai kara bunkasa kasuwar jari ta Najeriya tare da jawo karin masu zuba jari cikin harkar.
Kwairanga ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 14 ga Satumba, 2026, yayin taron “Facts Behind the Offer Presentation” na IPO na Dangote Refinery da kuma Opening Gong Ceremony, wanda aka gudanar a hedikwatar NGX da ke Marina, Lagos.
Ya ce wannan tayin hannayen jarin na Dangote Refinery shi ne mafi girma da aka taba gani a nahiyar Afirka, yana mai cewa hakan ya nuna irin muhimmancin kamfanin ga tattalin arzikin Najeriya da kasuwar jari.
A cewar Kwairanga, Dangote Refinery ta riga ta taka muhimmiyar rawa wajen sauya yanayin tattalin arzikin kasar, musamman a bangaren samar da man fetur. Ya ce sakamakon ayyukan matatar, Najeriya ta koma kasa mai fitar da tataccen man fetur zuwa kasashen waje, yayin da matsalar dogayen layukan man fetur ta ragu sosai.
Shugaban NGX Group ya kuma bayyana cewa ana sa ran fara wannan IPO zai haifar da gagarumar tasiri a kasuwar jari, musamman ta hanyar kara market capitalisation, yawan masu hannun jari, da kuma bunkasa yawan cinikayyar hannayen jari.
“Ganin irin sha’awar da ake nunawa kan wannan IPO, ina da yakinin cewa za mu ga gagarumin karin karfin kasuwar jari, yawan shareholders da kuma trading volumes da values,” in ji Kwairanga.
Ya kara da cewa ana sa ran kammala tayin da kuma daga bisani a jera kamfanin Dangote Refinery a kasuwar NGX a cikin kwata na hudu na shekarar 2026.
Kwairanga ya jaddada muhimmancin samar da cikakkun bayanai ga jama’a da masu zuba jari domin su fahimci kamfanin da kuma tsarin IPO kafin su yanke shawarar zuba jari.
A jawabinsa, ya tarbi Gwamnan Jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu, da shugaban Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote GCON, tare da sauran manyan baki da kwararrun harkokin kasuwar jari zuwa hedikwatar NGX.
Ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin mataki wajen wayar da kan jama’a kan kamfanin da kuma tsarin IPO, tare da bude sabon babi na dangantakar Dangote Refinery da kasuwar jari ta Najeriya.

Comments
Post a Comment