HON. YAKUBU SHEHU ABDULLAHI — ZABIN AL’UMMA
2027: Lokaci ne na cancanta, kwarewa da wakilci nagari.
Hon. Yakubu Shehu Abdullahi ya kasance ɗaya daga cikin mutanen da suka cancanci a ba su dama su jagoranci Kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu a ƙarƙashin jam’iyyar APC a shekarar 2027.
Jagoranci ba wai suna kawai ba ne; jagoranci yana buƙatar amincewar al’umma, kishin jama’a, hangen nesa da jajircewa wajen kare muradun waɗanda aka wakilta.
Muna da yakinin cewa Hon. Yakubu Shehu Abdullahi zai iya zama murya mai ƙarfi ga al’ummar Bauchi ta Kudu, tare da kawo wakilci mai ma’ana da kishin ci gaban yankin.
2027 — Lokaci ya yi da za a zaɓi cancanta.
Lokaci ya yi da za a zaɓi nagartaccen wakilci.
Lokaci ya yi da za a zaɓi Hon. Yakubu Shehu Abdullahi.
Da yardar Allah, idan al’umma suka ba shi dama, za su zaɓe shi, Insha Allah.
HON. YAKUBU SHEHU ABDULLAHI 2027
APC • Bauchi South • Sabon Ƙarfi, Sabon Wakilci
Allah Ya ba mu shugabanci na gari, Ya zaɓa mana mafi alheri.
✍️ Umar Umb Concept / Insight Tribune News

Comments
Post a Comment