HON. ABDULHAMID YAHAYA ABBA: GWARZON HIDIMAR AL’UMMA DA TUBALIN CIGABAN AREWA MASO GABAS


 


Daga Abdul Jazzy TV


A duk lokacin da ake magana kan matasa masu kishin kasa da kuma shugabanni masu kokarin kusantar gwamnati da jama’a, sunan Hon. Abdulhamid Yahaya Abba na daga cikin sunayen da ke fitowa fili saboda gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban al’umma.


A matsayinsa na Babban Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Hulɗa da Al’umma a Shiyyar Arewa Maso Gabas, ya nuna kwarewa, jajircewa da hangen nesa wajen hada kan jama’a da gwamnati domin tabbatar da cewa manufofi da shirye-shiryen ci gaba sun isa ga wadanda aka yi su dominsu.


Hon. Abdulhamid Yahaya Abba ya kasance mutum mai saukin kai, tausayi da mutunta kowa. Wannan hali nasa ya sa yake samun karbuwa da girmamawa daga matasa, dattawa da shugabanni a sassa daban-daban na kasar nan.


Ayyukansa sun kasance abin koyi ga matasa masu burin shiga harkar shugabanci, domin ya tabbatar cewa shugabanci na gari yana bukatar gaskiya, rikon amana, sadaukarwa da aiki tukuru domin amfanin jama'a.


Yayin da yake ci gaba da gudanar da ayyukan hidima ga kasa da al'umma, mutane da dama na yaba masa tare da yi masa addu'ar Allah Ya kara masa lafiya, hikima da nasara domin ya ci gaba da zama haske ga al'ummarsa da kuma Najeriya baki daya.


Hon. Abdulhamid Yahaya Abba na ci gaba da rubuta sunansa a tarihin shugabanci na gari ta hanyar hidima, jajircewa da kishin cigaban al'umma.

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

Prof. Hadiza Abdullahi Usman Celebrates Prof. Ahmed Ahidjo on Inaugural Lecture and Send-Forth

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS