GWAMNA UMAR NAMADI YA ZIYARCI RUBA DON TA'AZIYYA, YA NUNA TAUSAYI GA IYALAN MAMATAN


 


Daga Abba Goma | Insight Tribune News


A wani mataki da ya sake nuna kusancin gwamnati da al'umma, Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, FCA, ya kai ziyarar ta'aziyya a garin Ruba da ke Karamar Hukumar Kafin Hausa domin jajanta wa iyalai da al'ummar yankin bisa rasuwar wasu daga cikin 'ya'yansu.


Ziyarar wadda ta gudana a ranar Lahadi ta kasance wata alama ta tausayi, jajircewa da kuma nuna goyon baya ga al'ummar da ke cikin jimamin rashin masoyansu. Gwamna Umar Namadi ya bayyana alhininsa kan lamarin tare da addu'ar Allah Ya jikansu da rahama, Ya gafarta musu kura-kuransu, Ya kuma sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsu.


Hakazalika, gwamnan ya yi kira ga iyalai da daukacin al'ummar Ruba da su rungumi hakuri da juriya, yana mai tunatar da su cewa mutuwa hukuncin Allah ne da babu mai kauce masa.


Al'ummar yankin sun nuna godiya bisa wannan ziyara ta ta'aziyya, suna mai bayyana cewa kasancewar gwamnan a tsakaninsu a wannan lokaci na jimami ya kara musu kwarin gwiwa da jin cewa gwamnati na tare da su a kowane hali.


Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya jikan mamatan, Ya yalwata musu rahama, Ya gafarta musu zunubansu, Ya kuma ba iyalansu da 'yan uwansu hakurin jure wannan babban rashi. Amin.

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

Prof. Hadiza Abdullahi Usman Celebrates Prof. Ahmed Ahidjo on Inaugural Lecture and Send-Forth

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS