“Duniyar 2026 Ba Za Ta Ci Gaba da Tafiya da Tsarin Ƙarfin 1945 Ba” — Tinubu
Najeriya Ta Buƙaci Kujeru Biyu Na Dindindin Ga Afirka A Majalisar Tsaron MDD
By Umar Umb
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake ƙarfafa kiran da ake yi na sake fasalin tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya, yana mai cewa tsarin rarraba iko da aka gina a shekarar 1945 bai sake nuna ainihin yanayin duniya na shekarar 2026 ba.
Jawabin Shugaban Ƙasar a Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81 (UNGA 81) da aka gudanar a New York, an gabatar da shi ne a madadinsa daga Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.
Tinubu ya jaddada cewa Afirka ba za ta ci gaba da kasancewa a wajen teburin da ake yanke manyan shawarwarin duniya ba, alhali nahiyar na daga cikin yankunan da ayyukan Majalisar Tsaro suka fi shafa.
Najeriya ta nemi a bai wa Afirka aƙalla kujeru biyu na dindindin a Majalisar Tsaron MDD, tare da cikakken haƙƙin mamba na dindindin, ciki har da ikon veto idan har aka ci gaba da amfani da wannan tsarin, da kuma kujeru biyar marasa dindindin. Wannan bukata ta yi daidai da matsayin da Afirka ta dade tana gabatarwa a tattaunawar gyaran Majalisar Tsaro.
Diflomasiyya Maimakon Tilastawa
Najeriya ta sake tabbatar da cewa za ta ci gaba da fifita diflomasiyya, tattaunawa, haɗin gwiwa da dokokin ƙasa da ƙasa, maimakon tilastawa, ware ƙasashe ko amfani da ƙarfi ba bisa ka'ida ba.
Tinubu ya kuma bayyana aniyar Najeriya na ƙara taka rawa wajen samar da zaman lafiya da tsaro a Afirka, bisa tarihin ƙasar wajen ayyukan wanzar da zaman lafiya, sasanci da haɗin gwiwar tsaro.
Tattalin Arziki, Climate Change da Makamashi
A bangaren tattalin arziki, Najeriya ta danganta manufofinta na harkokin waje da gyare-gyaren tattalin arzikin cikin gida, tare da jaddada muhimmancin ƙarfafa hukumomi, saka hannun jari da bunƙasa kamfanoni masu zaman kansu.
Najeriya ta kuma yi kira da a samar da ƙarin tallafin kuɗi, fasaha da ƙwarewa ga ƙasashe masu tasowa domin tunkarar sauyin yanayi, yayin da ta sake bayyana burinta na cimma net-zero nan da 2060.
AI Da Makomar Matasa
Tinubu ya kuma yi kira da kada tsoron Artificial Intelligence (AI) ya hana duniya amfani da damar da fasahar ke da ita wajen inganta kiwon lafiya, ilimi, noma, shugabanci da tattalin arziki.
Najeriya ta gayyaci ƙasashen duniya da su ƙara haɗin gwiwa da matasan Afirka a fannin fasaha da kirkire-kirkire, tare da saka hannun jari a digital infrastructure, broadband, research da technology entrepreneurship.
AfCFTA Da Sabon Tsarin Tattalin Arzikin Afirka
Najeriya ta bayyana African Continental Free Trade Area (AfCFTA) a matsayin muhimmin ginshiƙi wajen sauya tattalin arzikin Afirka, tare da kira ga nahiyar ta ƙara mayar da hankali kan sarrafa albarkatun ƙasa a cikin gida, masana'antu, ƙirƙire-ƙirƙire da tattalin arzikin da ilimi ke jagoranta.
A fannin tsaro kuma, Najeriya ta jaddada muhimmancin musayar bayanan sirri, dakile hanyoyin samar da kuɗaɗen ta'addanci da safarar makamai ba bisa ƙa'ida ba, tare da ƙarfafa ilimi, damar tattalin arziki, shugabanci nagari da kare haƙƙin ɗan Adam.
Kira Kan Rikicin Sudan
Najeriya ta kuma yi kira da a gaggauta amfani da diflomasiyya wajen magance rikicin Sudan, tare da kare fararen hula, tabbatar da isar da agajin jin ƙai da kuma mutunta dokokin ƙasa da ƙasa.
A ƙarshe, Najeriya ta sake bayyana matsayinta na fifita haɗin gwiwa maimakon faɗa, tattaunawa maimakon rarrabuwar kai, fata maimakon tsoro, da haɗin kai maimakon warewa.
Kiran Najeriya na sake fasalin Majalisar Tsaro ya zo ne a daidai lokacin da Majalisar Ɗinkin Duniya kanta ke ci gaba da tattaunawa kan yadda za a samar da tsarin da zai fi wakiltar yanayin duniya na yau, musamman yadda Afirka ta kasance ba tare da mamba na dindindin a Majalisar Tsaro ba.
INSIGHT TRIBUNE NEWS
Abuja, Nigeria

Comments
Post a Comment