DAN KABIRU: JAGORANCI MAI KIMAR AMANA DA CI GABA
Ba a taɓa samun jagora da jagoranci mai kyau irin na Dan Kabiru, Hon. Kabiru Mu’azu Tarkunya, Chairman na Kauran Bauchi New GSM Village ba.
Jagorancinsa ya ginu ne bisa amincewa, tausayi, haɗin kai da kishin ci gaban al’umma. A ƙarƙashin jagorancinsa, ana ganin ƙoƙari wajen haɗa kan jama’a, kare muradun ‘yan kasuwa da kuma samar da kyakkyawar dangantaka tsakanin shugabanci da al’umma.
Dan Kabiru ba wai shugaba ne kawai ba, mutum ne da ya fahimci cewa jagoranci amana ne, kuma shugaba nagari shi ne wanda yake sauraron jama’arsa tare da neman mafita ga matsalolinsu.
Hakika, irin wannan jagoranci yana ƙara ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin al’umma. Hon. Kabiru Mu’azu Tarkunya ya kafa tarihi na jagoranci mai ma’ana a Kauran Bauchi New GSM Village.
Allah Ya ƙara masa basira, hikima da ƙarfin guiwa wajen ci gaba da yi wa al’umma hidima. 🤲

Comments
Post a Comment