2027: Takai/Sumaila — Hon. Abbas Uba Saraki Na Neman Wakiltar Al’umma a Majalisar Tarayya
A yayin da ake tunkarar babban zaben 2027, siyasar Sumaila/Takai Federal Constituency na kara samun sabon yanayi, yayin da Hon. Abbas Uba Saraki Kachako ke neman wakiltar al’ummar mazabar a Majalisar Wakilai ta Tarayya a karkashin jam’iyyar NDC. Rahotanni sun bayyana sunansa cikin jerin ‘yan takarar NDC na Takai/Sumaila.
Hon. Abbas Saraki, dan kasuwa kuma mai fafutukar ci gaban al’umma, ya bayyana manufofinsa kan ilimi, kiwon lafiya, samar da ayyukan yi ga matasa, tallafawa mata, noma da inganta ababen more rayuwa a Takai da Sumaila.
Haka kuma, ayyukan da aka danganta da shi sun hada da tallafin ilimi, gyaran makarantu, samar da kayan karatu da shirye-shiryen bunkasa sana’o’i da damar samun aikin yi ga matasa.
Yayin da 2027 ke kara matsowa, al’ummar Takai da Sumaila za su tantance manufofi, tarihin hidima da abubuwan da ‘yan takara suka gabatar, sannan su yanke shawarar wanda suke ganin zai fi dacewa ya wakilce su.
Takai/Sumaila 2027 — Hon. Abbas Uba Saraki, NDC.
By Umar Umb
Insight Tribune News

Comments
Post a Comment