WAZIRIN DAMBAM YA TAYA WAZIRIN MISAU MURNAR SAMUN SARAUTAR DAN GALADIMAN DAMBAM
Wazirin Dambam kuma Babban Mashawarcin Masarautar Dambam, Dr. Ahmad Umar Abdullahi, Ph.D, ya taya Wazirin Misau, Barrista Ahmed Ibrahim Dandijia, murnar samun sarautar Dan Galadiman Dambam da Mai Martaba Sarkin Dambam, Alhaji Idris Bappah Musa, ya tabbatar masa.
A cikin sakon taya murnar da ya fitar, Dr. Ahmad Umar Abdullahi ya bayyana cewa nadin Barrista Ahmed Ibrahim Dandijia a wannan matsayi babban abin alfahari ne ga Masarautun Dambam da Misau baki daya, la'akari da irin gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban al'umma, zaman lafiya da hadin kai.
Ya ce sarautar Dan Galadima na daga cikin manyan sarautun gargajiya masu daraja a kasar Hausa, wadda ke tattare da nauyin ba da shawara ga sarki, sasanta rikice-rikice da kuma taimakawa wajen tafiyar da harkokin masarauta.
Wazirin Dambam ya bayyana cewa wannan karramawa ta zo ne bisa cancanta da kuma irin ayyukan alheri da hidimar jama'a da Barrista Ahmed Ibrahim Dandijia ya dade yana yi, wanda hakan ya sa ya zama abin koyi ga al'umma da dama.
Ya yi addu'ar Allah Madaukakin Sarki Ya ba sabon Dan Galadiman Dambam hikima, lafiya da jagoranci na gari domin sauke nauyin wannan babban matsayi da aka dora masa, tare da ci gaba da amfani da mukaminsa wajen kawo cigaba da hadin kai a tsakanin al'umma.
Dr. Ahmad Umar Abdullahi ya kuma bukaci al'ummar Masarautar Dambam da na Misau da su bai wa sabon Dan Galadima cikakken hadin kai da goyon baya domin cimma manufofin ci gaban masarauta da walwalar jama'a.
A karshe, ya sake taya Barrista Ahmed Ibrahim Dandijia murna tare da fatan Allah Ya sanya wannan sarauta ta zama alheri gare shi, iyalansa da kuma al'ummar da yake yi wa hidima.
Daga Umar Umb
Insight Tribune News

Comments
Post a Comment