“Uwar-Gidana Ce Ta Biya Kuɗin Sadakin Aurena Da Amaryata” – Aminu Saira


Mashiryin shahararren fim ɗin Labarina, Malam Aminu Saira, ya bayyana irin gagarumar rawar da uwargidansa Aisha ta taka wajen cikar aurensa da sabuwar amaryarsa, Maryam, da ya aura a ƙarshen makon da ya gabata.


A wani saƙon godiya da ya wallafa a shafinsa na Facebook, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito, Aminu Saira ya yaba da karamci, mutunci da sadaukarwar da uwargidansa ta nuna masa a yayin shirye-shiryen auren.


“Karimci, mutunci da sadaukarwa na ƙarshe ƙurewa, Uwar-Gidana Aisha ta nuna a cikin hidimar aurena. Tun daga biyan sadaki da kuɗinta, ba da gudunmawa a dukkanin al’amura, har zuwa karɓar abokiyar zama hannu bibbiyu. Wannan ya ƙara mata daraja a idanuna da kuma idon amaryata da danginta,” in ji Saira.


Ya ƙara da cewa irin wannan hali na Aisha ya cancanci yabo da adalci daga kowane mutum mai kishin gaskiya da kyawawan ɗabi’u.


Haka kuma, Aminu Saira ya bayyana cewa ƙarin auren da ya yi ba saboda wata matsala da uwargidansa ba ce, sai dai saboda kyawawan halaye da nagartar da ya gani a sabuwar amaryarsa, Maryam.


“Na auri Maryam ne saboda nagarta da kyawawan halayenta da ta nuna tun daga farkon al’amari. Ina godiya ga Allah da Ya yi min wannan ni’ima. Ina fatan za mu ci gaba da tafiya a kan hanya madaidaiciya har zuwa gidan Aljannah,” in ji shi.


Kalaman Aminu Saira sun jawo ce-ce-ku-ce da martani iri-iri daga mabiyansa, inda da dama suka yaba da yadda ya fito fili ya nuna godiya ga uwargidansa bisa irin goyon bayan da ta ba shi.


Insight Tribune News
 

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

Prof. Hadiza Abdullahi Usman Celebrates Prof. Ahmed Ahidjo on Inaugural Lecture and Send-Forth

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS