Tawagar Ajiyan Sokoto Ta Kai Tallafin Abinci Ga Al’ummar Dinawa, Wurno LGA
Dinawa, Wurno LGA – Sokoto State
Tawagar da ke wakiltar Hon. Umaru Ajiya Isa (Ajiyan Sokoto) ta kai tallafin kayan abinci ga al’ummar garin Dinawa da ke Ƙaramar Hukumar Wurno ta Jihar Sokoto, waɗanda suka fuskanci iftila’in hare-haren barayin daji.
Tallafin ya zo ne domin rage raɗaɗin halin da mutanen yankin suka shiga sakamakon matsalolin tsaro da suka shafi rayuwarsu da hanyoyin samun abinci.
A yayin rabon tallafin, wakilan Ajiyan Sokoto sun bayyana cewa wannan taimako na daga cikin ƙoƙarin da yake yi na tallafawa al’umma musamman waɗanda suka shiga mawuyacin hali. Sun jaddada cewa Ajiyan Sokoto na ci gaba da nuna damuwa da kula da jin daɗin jama’a ba tare da la’akari da nisan wuri ko yanayin da ake ciki ba.
Al’ummar Dinawa sun nuna farin ciki tare da miƙa godiyarsu ga Ajiyan Sokoto bisa wannan karamci, suna masu bayyana cewa tallafin zai taimaka wajen rage musu wasu daga cikin ƙalubalen da suke fuskanta.
Masu lura da al’amuran yankin sun bayyana wannan mataki a matsayin abin a yaba, wanda ke nuna kishin jama’a da kulawa da walwalar al’umma.
Ajiyan Sokoto – Jagora Mai Tausayi, Mai Taimakon Jama’a, Kuma Mai Kula Da Bukatun Al’umma.
.jpg)
Comments
Post a Comment