SENATOR SHEHU BUBA UMAR: Jagoran Da Yake Da Kwarewa, Hangen Nesa Da Cancantar Jagorantar Bauchi A 2027
Daga Hajiyah Zainab Aliyu Yusuf Support Group for Shehu Buba Umar
A duk lokacin da al'umma ke neman shugaba nagari, abin da suke dubawa shi ne gaskiya, kwarewa, jajircewa da kuma tarihin hidima ga jama'a. A yau, mutane da dama a fadin Jihar Bauchi suna kallon Sanata Shehu Buba Umar a matsayin daya daga cikin shugabannin da suka cancanci a damka musu ragamar jagorancin jihar a shekarar 2027.
Sanata Shehu Buba Umar, mai wakiltar Bauchi ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya, ya shahara wajen sadaukar da kai ga ci gaban jama'a, zaman lafiya da bunkasa tattalin arziki. Kafin zamansa Sanata, ya yi aiki a fannoni daban-daban na gwamnati da shugabanci, tare da samun gogewa a harkokin gudanarwa da warware rikice-rikice. Haka kuma yana da digiri a fannin Adult Education daga Jami'ar Ahmadu Bello da kuma digiri na biyu a fannin Peace and Conflict Resolution daga Jami'ar Jos.
A matsayinsa na Sanata, ya kasance mai ba da gudunmawa wajen samar da tsaro, zaman lafiya da ayyukan ci gaba ga al'ummarsa. Tarihinsa na shugabanci da kusancinsa da talakawa ya sa mutane da yawa ke ganin yana da hangen nesan da zai iya kai Bauchi zuwa wani sabon mataki na ci gaba.
Kungiyar Hajiyah Zainab Aliyu Yusuf Support Group for Shehu Buba Umar na da yakinin cewa idan aka ba Sanata Shehu Buba Umar damar jagorantar Jihar Bauchi a karkashin jam'iyyar PRP a 2027, zai yi amfani da iliminsa, kwarewarsa da gogewarsa wajen inganta rayuwar al'umma, samar da damammaki ga matasa da mata, da kuma kara habaka ci gaban jihar baki daya.
Bauchi na bukatar shugabanci mai hangen nesa, shugabanci mai kusanci da jama'a, da shugabanci mai mayar da hankali kan ci gaba. A cewar mambobin wannan kungiyar, Sanata Shehu Buba Umar na daga cikin mutanen da suka mallaki wadannan siffofi.
Sabuwar Bauchi, Sabon Zamani – Tare da Shehu Buba Umar.

Comments
Post a Comment