NAGARTA DA JAJIRCEWA: DALILAN DA KE KARA KARFIN GOYON BAYAN AJIYAN SOKOTO A SOKOTO EAST
Dr. Umaru Ajiya Isa, wanda aka fi sani da Ajiyan Sokoto, na ci gaba da samun karɓuwa da goyon baya daga jama'a da masu ruwa da tsaki a siyasar Jihar Sokoto sakamakon nagarta, jajircewa da kuma tarihin hidimar da ya yi wa al'umma tsawon shekaru. A matsayinsa na gogaggen shugaba kuma ƙwararren masani a harkokin kuɗi, mutane da dama na kallonsa a matsayin mutum mai hangen nesa wanda zai iya kawo wakilci nagari ga al'ummar Sokoto East a Majalisar Dattawan Najeriya.
A cikin 'yan watannin nan, Ajiyan Sokoto ya samu gagarumar goyon baya daga shugabannin Jam'iyyar APC, dattawa, matasa da sauran al'ummomin yankin Sokoto East, lamarin da ya haifar da bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Sanata domin wakiltar mazabar. Masu goyon bayansa na bayyana cewa ƙwarewarsa a manyan mukaman gwamnati da kuma ayyukan alheri da ya dade yana yi sun sanya ya zama zabin da ya dace don jagorantar yankin zuwa ci gaba mai ɗorewa.
Ajiyan Sokoto ya jaddada cewa babban burinsa shi ne tabbatar da tsaro, inganta ilimi, ƙarfafa matasa da mata, da kuma samar da ayyukan raya ƙasa da za su amfani al'ummar Sokoto East baki ɗaya. Ya kuma bayyana aniyarsa ta yin aiki tare da gwamnatin tarayya da ta jiha domin tabbatar da cewa yankin ya samu rabonsa na ayyukan ci gaba da abubuwan more rayuwa.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun yi imanin cewa irin karɓuwar da Ajiyan Sokoto ke samu a tsakanin al'umma na nuna yadda jama'a ke ƙara neman shugabanci mai nagarta, gaskiya da rikon amana. Haka kuma, an bayyana cewa ya samu amincewar masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC a matsayin ɗaya daga cikin fitattun jagororin da za su iya ɗaga martabar mazabar Sokoto East a matakin ƙasa.
Yayin da ake tunkarar zaɓukan 2027, magoya bayan Ajiyan Sokoto na ci gaba da bayyana kwarin gwiwarsu cewa ƙwarewa, mutunci, tausayi da sadaukarwa ga jama'a za su kasance manyan ginshiƙan nasarar sa. A cewarsu, samun Ajiyan Sokoto a matsayin jagoran APC kuma wakilin Sokoto East a Majalisar Dattawa zai buɗe sabon babi na ci gaba, haɗin kai da wakilci mai inganci ga al'ummar yankin.
A bisa wannan dalilai, mutane da dama na kallon Ajiyan Sokoto a matsayin jagora mai hangen nesa wanda zai iya zama muryar talakawa, mai kare muradun al'umma da kuma wakilin da zai kawo sauyi mai ma'ana ga Sokoto East da Najeriya baki ɗaya.

Comments
Post a Comment