HAJIYAH ZAINAB ALIYU YUSUF SUPPORT GROUP FOR SHEHU BUBA UMAR TA YI KIRA GA AL’UMMAR BAUCHI SU MARAWA PRP BAYA DOMIN GINA SABUWAR JIHAR BAUCHI A 2027
Kungiyar Hajiyah Zainab Aliyu Yusuf Support Group for Shehu Buba Umar ta yi kira ga al’ummar Jihar Bauchi da su hada kai tare da marawa jam’iyyar PRP baya domin tabbatar da gina sabuwar Bauchi mai cike da ci gaba, adalci da walwalar jama’a a zaben shekarar 2027.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta bayyana cewa lokaci ya yi da al’ummar jihar za su rungumi shugabanci nagari da zai fifita muradun jama’a, bunkasa ilimi, kiwon lafiya, noma, samar da ayyukan yi ga matasa da kuma inganta tsaro a fadin jihar.
Kungiyar ta nuna cikakken goyon bayanta ga Sanata Shehu Buba Umar, tana mai bayyana shi a matsayin jagora mai hangen nesa, kwarewa da kishin talakawa, wanda zai iya jagorantar jihar zuwa sabon matakin ci gaba da wadata.
Hajiyah Zainab Aliyu Yusuf ta kuma yi kira ga mata, matasa da sauran al’ummar Bauchi da su tashi tsaye wajen wayar da kan jama’a tare da shiga harkokin siyasa domin tabbatar da nasarar PRP da Sanata Shehu Buba Umar a zaben 2027.
Kungiyar ta jaddada cewa hadin kai, zaman lafiya da goyon bayan jama’a ne ginshikin nasarar kowace al’umma, tare da bayyana cewa lokaci ya yi da za a gina “Sabuwar Bauchi” wadda za ta anfani kowa ba tare da nuna bambanci ba.
SPONSORED

Comments
Post a Comment