GOMBE 2027: LOKACIN DA CANCANTA ZA TA YI MAGANA
A duk lokacin da ake magana kan makomar Jihar Gombe a 2027, akwai sunayen da ke fitowa saboda cancanta, kwarewa da irin gudunmawar da suka bayar ga al'umma. Daya daga cikin irin wadannan mutane shi ne Prof. Isa Ali Ibrahim Pantami.
A cewar Sale Muhammed, Adon Garin Funakaye, al'umma na bukatar shugaba mai ilimi, hangen nesa, gaskiya da kishin ci gaban jama'a. Ya bayyana cewa Prof. Pantami ya gina tarihin da ya sa mutane da dama ke kallonsa a matsayin jagora mai iya kawo sauyi mai amfani ga jihar.
"Ba maganar son rai ko kame-kame ba ce. Idan aka yi la'akari da ilimi, kwarewa, gogewa da jajircewa wajen hidimtawa al'umma, Prof. Isa Ali Pantami na cikin mutanen da suka cancanci a ba su dama su jagoranci Gombe zuwa sabon matakin ci gaba," inji Sale Muhammed.
Ya kara da cewa matasa, mata da masu sana'o'i na bukatar shugabanci mai mayar da hankali kan bunkasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da inganta rayuwar jama'a, yana mai cewa irin wadannan manufofi ne suka sa mutane da yawa ke nuna amincewa da Pantami.
A karshe, Sale Muhammed ya yi kira ga al'ummar Jihar Gombe da su ci gaba da sanya cancanta, nagarta da kishin jama'a a gaba yayin zabar shugabanni, domin hakan ne zai tabbatar da ci gaba mai dorewa ga jihar.

Comments
Post a Comment