CANCANTA DA DACEWA SU AKE MAGANA, BA KAME-KAME BA: PROF. ISA ALI PANTAMI SHI YA FI CANCANTA YA ZAMA GWAMNAN GOMBE A 2027 – SALE MUHAMMED, ADON GARIN FUNAKAYE
A siyasa, abin da al'umma ke nema shi ne shugaba mai ilimi, hangen nesa, kwarewa da nagartar gudanarwa. Idan aka zo maganar wanda ya fi cancanta ya jagoranci Jihar Gombe a shekarar 2027, sunan Prof. Isa Ali Ibrahim Pantami na daga cikin sunayen da ke fitowa karara saboda irin gudunmawar da ya bayar a matakan kasa da na duniya. Ya taba zama Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani na Najeriya, sannan ya jagoranci manyan cibiyoyin fasaha da ci gaban zamani a kasar nan.
A cewar Sale Muhammed, Adon Garin Funakaye, "Cancanta da dacewa su ake magana, ba kame-kame ba. Kowa ya san Prof. Isa Ali Pantami mutum ne mai ilimi, kishin al'umma da hangen nesa. Ya nuna bajinta a duk inda ya samu dama, kuma babu shakka zai iya kawo sabon salo na ci gaba da inganta rayuwar al'ummar Gombe."
Ya kara da cewa Gombe na bukatar shugaba mai fahimtar zamani, mai iya jawo ci gaba, saka hannun jari, bunkasa ilimi da samar da damar yi wa matasa aiki. A cewarsa, tarihin Prof. Pantami a fannin ilimi, fasaha da shugabanci ya sanya ya zama daya daga cikin fitattun 'ya'yan Gombe da suka yi fice a duniya.
Sale Muhammed ya yi kira ga al'ummar Jihar Gombe da su ci gaba da duba cancanta, gaskiya da nagarta wajen zaben shugabanni, yana mai jaddada cewa Prof. Isa Ali Pantami na da dukkanin siffofin da za su taimaka wajen kai jihar zuwa mataki na gaba na ci gaba da bunkasa tattalin arziki.
"Lokacin zaben shugaba ya zo, cancanta ce ta kamata ta yi magana. Kuma idan aka yi maganar cancanta, Prof. Isa Ali Pantami na daga cikin fitattun wadanda suka dace da jagorantar Jihar Gombe a 2027," inji Sale Muhammed, Adon Garin Funakaye.

Comments
Post a Comment