Bala Wunti Ya Samu Sabon Muƙami a Fannin Makamashi na Duniya
Wani sabon ci gaba mai muhimmanci ya samu a fannin makamashi bayan da aka zaɓi fitaccen ƙwararren masanin makamashi na Najeriya, Bala Wunti, domin ya jagoranci ayyukan World Energy Council Nigeria a matsayin Babban Jami'in Gudanarwa (CEO).
Wannan naɗi ya zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke ƙara samun karɓuwa a matakin duniya wajen tattaunawa da tsara manufofin makamashi. Hakan ya biyo bayan amincewar World Energy Council da kafa cikakken kwamitinta a Najeriya, wanda zai kasance wata muhimmiyar gada tsakanin ƙasar da manyan masu ruwa da tsaki a fannin makamashi na duniya.
Masana na kallon wannan ci gaba a matsayin wata dama da za ta bai wa Najeriya damar ƙara bayyana ra'ayoyinta kan batutuwan tsaron makamashi, sauyin yanayi da hanyoyin samar da makamashi mai ɗorewa ga al'umma.
Da yake bayyana hangen nesansa, Bala Wunti ya jaddada aniyarsa ta ƙarfafa haɗin gwiwa da masu zuba jari tare da samar da hanyoyin da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki ta hanyar ingantaccen tsarin makamashi.
Kafin wannan naɗi, Bala Wunti ya yi fice a masana'antar makamashi ta Najeriya, inda ya riƙe manyan muƙamai a NNPC Ltd tare da ba da gudunmawa wajen ci gaban harkokin makamashi a ƙasa da ma nahiyar Afirka.
Masu ruwa da tsaki na ganin cewa wannan sabon nauyi da aka ɗora masa zai taimaka wajen ƙara ɗaga martabar Najeriya a tattaunawar makamashi ta duniya da kuma buɗe ƙofofin sabbin damammaki ga ƙasar.
UMAR UMB

Comments
Post a Comment