An Naɗa Dr. Bala Maijama’a Wunti Cikin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC


 Daga Umar Umb | Insight Tribune News


An yi maraba da naɗa Dr. Bala Maijama’a Wunti a matsayin ɗaya daga cikin mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.


Masu ruwa da tsaki da magoya bayansa sun bayyana wannan naɗi a matsayin wata gagarumar shaida ta amincewa da ƙwarewarsa, nagartarsa a shugabanci da kuma gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban al’umma da ƙasa baki ɗaya.


Kwamitin yaƙin neman zaɓen na APC wanda aka kafa domin jagorantar shirye-shiryen jam’iyyar a faɗin ƙasar nan ya haɗa manyan jiga-jigan siyasa, ƙwararru da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓen 2027.


Masu goyon bayan Dr. Wunti sun bayyana cewa wannan dama ce da za ta ƙara ba shi damar amfani da gogewarsa, hikimarsa da kuma kyakkyawar alaƙarsa da jama’a wajen ƙarfafa manufofin jam’iyyar da bunƙasa ayyukan yaƙin neman zaɓe.


Sun kuma taya shi murnar wannan sabon matsayi tare da nuna kwarin gwiwa cewa zai ci gaba da bayar da gudunmawa mai ma’ana wajen inganta dimokuraɗiyya, haɗin kai da ci gaban Najeriya.


Masu sharhi kan harkokin siyasa sun yi amannar cewa wannan naɗi ya ƙara tabbatar da matsayin Dr. Bala Maijama’a Wunti a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ‘yan Najeriya masu tasiri da ke ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen hidimtawa al’umma da ƙasa baki ɗaya.

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

Prof. Hadiza Abdullahi Usman Celebrates Prof. Ahmed Ahidjo on Inaugural Lecture and Send-Forth

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS