Ajiyan Sokoto Ya Tallafawa ’Yan Gudun Hijira Da Abinci A Isa Da Sabon Birni
Daga Insight Tribune News
Dan Takarar Kujerar Sanatan Sokoto ta Gabas a karkashin jam’iyyar APC, Dr. Umaru Ajiya (Ajiyan Sokoto), ya gudanar da rabon tallafin abinci ga ’yan gudun hijira a kananan hukumomin Isa da Sabon Birni, wadanda hare-haren ’yan ta’adda suka tilastawa barin garuruwansu da kauyukansu.
Shirin tallafin ya gudana cikin tsari da lumana, inda aka rabawa daruruwan iyalai kayan abinci domin rage musu radadin halin da suke ciki sakamakon matsalolin rashin tsaro da suka fuskanta.
Wadanda suka amfana da tallafin sun bayyana matukar godiyarsu ga Ajiyan Sokoto bisa wannan taimako na jin kai, suna mai cewa tallafin ya zo a daidai lokacin da suke cikin bukata.
Masu ruwa da tsaki a yankunan Isa da Sabon Birni sun yabawa Dr. Umaru Ajiya saboda irin kulawar da yake nunawa ga marasa galihu da wadanda bala’in rashin tsaro ya shafa, tare da bayyana cewa irin wadannan ayyuka na taimakawa wajen dawo da fata da kwarin gwiwa ga al’umma.
Al’ummar yankunan sun yi addu’ar Allah Ya saka masa da mafificin alheri, Ya kara masa lafiya, arziki da nasara a dukkan ayyukansa na hidimtawa jama’a.
— Insight Tribune News


Comments
Post a Comment