AJIYAN SOKOTO YA ALHINI DA RASUWAR SALLAMAN GARKUWAN SOKOTO
Dan takarar Sanatan Sokoto ta Gabas a karkashin jam’iyyar APC, Dr. Umaru Ajiya Isa (Ajiyan Sokoto), ya bayyana alhininsa tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalai, al’umma da masarautar Sokoto bisa rasuwar Alhaji Yakubu Isa (Sallaman Garkuwan Sokoto).
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na yakin neman zabensa, Buhari Auwalu Gada, ya fitar, Ajiyan Sokoto ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ba ga iyalansa kadai ba, har ma da karamar hukumar Isa da daukacin al’ummar Musulmi.
Ya bayyana marigayi Sallaman Garkuwan Sokoto a matsayin jajirtaccen jagoran al’umma wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidima da ci gaban jama’arsa. Ya ce gudummawar da ya bayar a rayuwarsa za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa ga al’umma masu zuwa.
Dr. Umaru Ajiya ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin, Ya yalwata masa rahama tare da sanya shi cikin Aljannatul Firdaus. Haka kuma ya bukaci iyalai da ‘yan uwa da su yi hakuri tare da karbar hukuncin Allah, yana mai jaddada cewa mutuwa wata gaskiya ce da babu wanda zai kauce mata.
“Mu a matsayinmu na Musulmi dole ne mu kasance masu cikakken imani da nufin Allah, domin Shi ne Mai bayar da rai kuma Mai karbar sa a lokacin da Ya ga dama,” in ji Ajiyan Sokoto.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da mara wa iyalan marigayin baya tare da yi musu addu’o’i domin samun saukin wannan babban rashi.
Marigayi Alhaji Yakubu Isa (Sallaman Garkuwan Sokoto) ya rasu ranar Juma’a, 7 ga Agustan 2026, kuma an yi jana’izarsa bisa koyarwar addinin Musulunci.
Allah Ya jikansa da rahama, Ya sanya Aljanna ta zama makomarsa. Amin.

Comments
Post a Comment