AIG AUWAL MUSA MUHAMMAD YA ZAMA SABON COMMANDANT NA NIGERIA POLICE ACADEMY, WUDIL
Hukumar Police Service Commission (PSC) ta amince da naɗin AIG Auwal Musa Muhammad a matsayin sabon Commandant na Nigeria Police Academy (POLAC), Wudil da ke Jihar Kano.
AIG Auwal Musa Muhammad ƙwararren jami’in ɗan sanda ne mai sama da shekaru 33 yana hidima a fannoni daban-daban da suka haɗa da gudanar da ayyukan tsaro, bincike, tattara bayanan sirri da horas da jami’an ‘yan sanda. Kafin wannan naɗi, ya riƙe muƙamai da dama masu muhimmanci ciki har da Kwamandan Police College Maiduguri, Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Bauchi da kuma Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (AIG) a shiyyoyi daban-daban na ƙasar nan.
Masu ruwa da tsaki na kallon wannan naɗi a matsayin wani muhimmin mataki da zai taimaka wajen ƙara inganta horo, ɗabi’a da ƙwarewar jami’an ‘yan sanda masu tasowa a Nigeria Police Academy.
Ana sa ran sabon Commandant ɗin zai kawo sabbin tsare-tsare da za su ƙara bunƙasa aikin horas da jami’an ‘yan sanda tare da ƙarfafa martabar POLAC a matsayin babbar cibiyar koyar da aikin ‘yan sanda a Najeriya.

Comments
Post a Comment