'Yan Takarar Jam'iyyar ADC na Jihar Jigawa Sun Gudanar da Muhimmin Taro a Dutse



 Daga Hussaini Muhammad Tsakuwawa

Dutse, Jihar Jigawa – 'Yan takarar Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Jigawa sun gudanar da muhimmin taro a Birnin Dutse domin tattauna manyan batutuwan da suka shafi ci gaban jam'iyya, ƙarfafa haɗin kai, da tsara dabarun tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.


Taron ya gudana ƙarƙashin jagorancin jigo kuma jagora a Jam'iyyar ADC, Hon. Auwal Ibrahim Sansani (CNA), ɗan takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Jigawa mai wakiltar Miga Constituency. Mahalarta taron sun jaddada muhimmancin haɗin kai, gaskiya, riƙon amana da jajircewa wajen yi wa al'umma hidima domin tabbatar da cigaba mai ɗorewa ga jihar Jigawa.


An kuma tattauna hanyoyin ƙarfafa tubalin jam'iyyar a matakai daban-daban tare da ƙarfafa zumunci da haɗin gwiwa tsakanin mambobi domin cimma manufofin da aka sa gaba.


A ƙarshen taron, mahalarta sun yi addu'ar neman taimakon Allah Maɗaukakin Sarki da Ya ba Jam'iyyar ADC nasara, Ya ba 'yan takararta ikon sauke nauyin da al'umma za ta ɗora musu, tare da tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da cigaba a Jihar Jigawa da Najeriya baki ɗaya.


Insight Tribune News ta ruwaito cewa taron na nuna ƙudurin jam'iyyar na ƙara ƙarfafa tsarinta da kuma shirye-shiryen fuskantar zaɓen shekarar 2027 cikin haɗin kai da manufa ɗaya.

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

Prof. Hadiza Abdullahi Usman Celebrates Prof. Ahmed Ahidjo on Inaugural Lecture and Send-Forth

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS