WAZIRIN DAMBAM: JIGO MAI KISHIN AL’UMMA DA GINA KASA
Mai Martaba Sarkin Dambam ya bayyana Wazirin Dambam a matsayin mutum nagari, mai kima da mutunci, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa al’umma da tallafa wa ci gaban kasa.
Sarkin ya bayyana hakan ne a yayin bikin nadin Dr. Ahmad Umar a matsayin 1st Jagaban Misau, inda ya yaba da irin gudunmawar da Wazirin Dambam ke bayarwa wajen bunkasa zaman lafiya, hadin kai da ci gaban al’umma.
Hakazalika, Mai Martaba Sarkin Misau ya bayyana Wazirin Dambam a matsayin jigo mai hangen nesa, wanda ayyukansa da shawarwarinsa ke taimakawa wajen inganta rayuwar jama’a da karfafa cigaban kasa. Ya ce irin wadannan mutane ne ke da muhimmiyar rawa wajen gina al’umma mai dorewa da samar da kyakkyawar makoma ga matasa masu tasowa.
Masarautun biyu sun jaddada cewa nagarta, rikon amana, tausayi da kishin kasa da Wazirin Dambam ke nunawa sun sanya ya zama abin koyi ga al’umma, tare da tabbatar da cewa irin gudunmawarsa za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa a tarihin ci gaban yankin da kasa baki daya.
— Umar Umb
Insight Tribune News

Comments
Post a Comment