Nagarta, Cancanta da Tausayi: Hajiyah Zainab Aliyu Yusuf (Maman Abba), Gwarziyar Mace Mai Kima


 A duk lokacin da ake magana kan mata masu nagarta, cancanta da kuma zuciyar tausayi a Jihar Bauchi, sunan Hajiyah Zainab Aliyu Yusuf (Maman Abba) na daga cikin sunayen da ke haskakawa. Ta kasance mace mai mutunci, dattako da kishin al'umma, wacce ta sadaukar da lokacinta wajen taimakawa mabukata da karfafa gwiwar mata da matasa.


Maman Abba, wacce ita ce matar Sanatan Bauchi ta Kudu kuma ɗan takarar kujerar Gwamnan Jihar Bauchi a jam'iyyar PRP na shekarar 2027, Sanata Shehu Buba Umar, ta zama abin koyi ga mata da yawa saboda kyawawan dabi'unta, karamci da tausayi ga al'umma. Sanata Shehu Buba Umar dai ya samu tikitin takarar gwamnan Bauchi a karkashin jam'iyyar PRP domin zaben 2027.


Ta hanyar kyakkyawar mu'amala da tausayi, Hajiyah Zainab ta gina kyakkyawar alaka da al'umma, inda mutane da dama ke kallonta a matsayin uwa mai kula da jin dadin jama'a. Nagarta da karamcinta sun sanya ta zama abin alfahari ga iyalai, mata da matasan da suke amfana da shawarwari da goyon bayanta.


Hakika, arzikin samun mace mai hali irin na Hajiyah Zainab Aliyu Yusuf (Maman Abba) wata ni'ima ce ga al'umma, domin tana nuna cewa shugabanci ba wai iko kawai ba ne, har ma da tausayi, adalci da kula da rayuwar jama'a.


Insight Tribune News

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

Prof. Hadiza Abdullahi Usman Celebrates Prof. Ahmed Ahidjo on Inaugural Lecture and Send-Forth

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS