Muhimmancin Fasaha da Haɗa Ilimin Zamani da Na Addini Domin Gina Al’umma Mai Cigaba – Inji Dan Adalan Mubi, Malam Musa Jidda
Dan Adalan Mubi, Malam Musa Jidda, ya jaddada muhimmancin rungumar fasahar zamani tare da riƙo da ilimin addini domin gina al’umma mai nagarta, ci gaba da kuma samun makoma mai haske.
Malam Musa Jidda ya bayyana cewa duniya ta shiga wani zamani da ilimi da fasaha suka zama ginshiƙan ci gaban ƙasashe da al’umma. Ya ce matasa su dage wajen neman ilimin zamani kamar kimiyya, fasahar sadarwa, kiwon lafiya, noma da sauran fannoni masu amfani, domin su kasance cikin masu bada gudunmawa ga ci gaban ƙasa.
Sai dai ya yi gargadin cewa duk wani ilimi ko fasaha da ba a gina ta bisa kyawawan ɗabi’u da koyarwar addini ba, na iya haifar da matsaloli ga al’umma. Saboda haka ya ce wajibi ne a haɗa ilimin zamani da na addini domin samar da mutane masu ilimi, tarbiyya, gaskiya da kishin ƙasa.
“Fasaha wata babbar ni’ima ce idan aka yi amfani da ita ta hanyar da ta dace. Yakamata matasa su yi anfani da ita wajen neman ilimi, bunƙasa kasuwanci, ƙirƙire-ƙirƙire da kuma inganta rayuwar al’umma, ba wajen yaɗa miyagun ɗabi’u ko ɓata lokaci ba,” in ji Malam Musa Jidda.
Ya ƙara da cewa ci gaban kowace al’umma yana dogara ne da yadda take bai wa ilimi muhimmanci, tare da kiyaye kyawawan ɗabi’u da darajojin addini. Ya yi kira ga iyaye, malamai da shugabanni da su ƙara himma wajen tarbiyyantar da matasa domin su zama shugabannin gobe masu kishin ƙasa da tsoron Allah.
A ƙarshe, Dan Adalan Mubi ya yi addu’ar Allah Ya ba Najeriya da sauran al’ummomin duniya zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa, tare da bai wa matasa damar amfani da ilimi da fasaha wajen gina makoma mai kyau ga kansu da ƙasarsu.

Comments
Post a Comment