Mai Martaba Sarkin Dambam Ya Nada ’Ya’yan Wazirin Dambam da Sarautun Gargajiya


 Masarautar Dambam ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Dambam, Alhaji Bappah Idris Musa Suleiman, ta gudanar da bikin naɗin sarauta ga wasu daga cikin ’ya’yan gidan Wazirin Dambam, lamarin da ya jawo farin ciki da taya murna daga al’umma da masoya masarautar.


Sabbin masu sarautun da aka naɗa sun haɗa da:


Muhammad Ahmad Umar (Falalu) – Barayan Dambam


Umar Ahmad Umar (Faruqu) – Makama Babban Dambam


Muhammadu Ahmad Umar – Dan Jikan Dambam


Muhammad Ahmad Umar – Dan Giwan Dambam


Abubakar Ahmad Umar – Falakin Dambam


Khadija Idris Bappha Musa – Gimbiyar Dambam



An gudanar da bikin naɗin sarautar a Fadar Mai Martaba Sarkin Dambam a ranar Asabar, 11 ga Yulin 2026, inda manyan baƙi, masu sarauta, ’yan uwa da abokan arziki suka halarta domin shaida wannan gagarumin biki.


Al’umma da dama sun bayyana cewa naɗin sarautun ya zo ne a matsayin girmamawa ga gudunmawar iyalan Wazirin Dambam wajen ci gaba, haɗin kai da kuma martabar Masarautar Dambam. Haka kuma, sun yi addu’ar Allah Ya ba sabbin masu sarautun hikima da nasarar gudanar da nauyin da aka ɗora musu. 


— Insight Tribune News

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

Prof. Hadiza Abdullahi Usman Celebrates Prof. Ahmed Ahidjo on Inaugural Lecture and Send-Forth

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS