JITA-JITAR CEWA DR. BALA MAIJAMA’A WUNTI ZAI ZAMA DG NA KAMFEN ƊIN WANI ƊAN TAKARAR GWAMNA A BAUCHI BA TA DA TUSHE — UMAR UMB



 An bayyana rahotannin da ke yawo a wasu kafafen sada zumunta na cewa Dr. Bala Maijama’a Wunti zai zama Darakta Janar (DG) na kamfen ɗin wani ɗan takarar gwamna a Jihar Bauchi a matsayin jita-jita marar tushe.


Da yake martani kan batun, Umar Umb ya ce babu wani sahihin bayani da ke nuna cewa Dr. Bala Maijama’a Wunti ya amince ko kuma yana da niyyar karɓar irin wannan matsayi.


“Dr. Bala Maijama’a Wunti sananne ne wajen ayyukan alkhairi, tallafa wa marasa galihu, bunƙasa ilimi, lafiya da ƙarfafa rayuwar al’umma. Wannan shi ne abin da ya sa ya samu karɓuwa da girmamawa a tsakanin jama’a,” in ji Umar Umb.


Ya ƙara da cewa a halin yanzu babban burin Dr. Bala Maijama’a Wunti shi ne ci gaba da gudanar da ayyukan jin ƙai da tallafawa ci gaban al’umma, tare da bayar da goyon baya ga Shugaban Ƙasa, Mai Girma Bola Ahmed Tinubu, domin samun damar ci gaba da aiwatar da manufofin da ke kawo cigaba da walwala ga ‘yan Najeriya.


Umar Umb ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da duk wani labari da ba a tabbatar da sahihancinsa ba, yana mai jaddada cewa Dr. Bala Maijama’a Wunti ya fi karkata ga ayyukan alheri da ci gaban al’umma fiye da shiga cece-kuce ko jita-jitar siyasa.


— Insight Tribune News

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

Prof. Hadiza Abdullahi Usman Celebrates Prof. Ahmed Ahidjo on Inaugural Lecture and Send-Forth

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS