JIGAWA TA TSAKIYA: 'YAN TAKARAR ADC SUN HAƊU A KANO, SUN ƘUDURI ANIN SAMUN NASARA A ZAƁEN 2027
A wani muhimmin mataki na ƙarfafa haɗin kai da tsara ingantattun dabarun siyasa, manyan 'yan takarar Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) na yankin Jigawa ta Tsakiya sun gudanar da zama na musamman a Birnin Kano domin tattauna hanyoyin da za su ƙara wa jam'iyyar ƙarfi gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Taron ya gudana ƙarƙashin jagorancin Alhaji Ahmad Isah Dan Barayan Dutse, ɗan takarar Sanatan Jigawa ta Tsakiya, tare da halartar Hon. Muhammad Naziru Jahun (Dan Gadawa), ɗan takarar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Miga/Jahun Federal Constituency, da Hon. Auwal Ibrahim Sansani (CNA), ɗan takarar Majalisar Dokokin Jihar Jigawa mai wakiltar Miga Constituency.
A yayin taron, mahalarta sun tattauna kan hanyoyin ƙarfafa haɗin kan jam'iyya, tsara dabarun siyasa masu inganci, da kuma yadda za a ƙara kusantar al'umma tare da gabatar da manufofin da za su taimaka wajen bunƙasa rayuwar jama'a.
Sun jaddada cewa haɗin kai, jajircewa, gaskiya da kusanci da jama'a su ne manyan ginshiƙan da za su jagoranci tafiyar ADC a yankin Jigawa ta Tsakiya, tare da nuna aniyarsu ta ci gaba da gudanar da siyasa cikin lumana, adalci da mutunta ra'ayoyin al'umma.
Taron ya ƙare cikin yanayi na fahimtar juna da ƙarfafa zumunci tsakanin shugabannin jam'iyyar, inda suka yi kira ga magoya baya da masu ruwa da tsaki da su ci gaba da haɗa kai domin gina jam'iyya mai ƙarfi da kuma cimma burin da aka sanya a gaba.
SPONSOR Hussaini Tsakuwawa



Comments
Post a Comment