Hussaini Tsakuwawa Ya Godewa Hon. Muhammad Naziru Jahun (Dan Gadawa) Kan Ziyarar Ta'aziyya a Hantsu
Hussaini Tsakuwawa ya miƙa saƙon godiya na musamman ga ɗan takarar da yake marawa baya, Hon. Muhammad Naziru Jahun (Dan Gadawa), bisa karamci, tausayi da jajircewar da ya nuna ta hanyar kai ziyarar ta'aziyya zuwa garin Hantsu a wannan lokaci na jimami.
A cewarsa, ziyarar ta Hon. Muhammad Naziru Jahun ta kasance abin ƙarfafawa da sanyaya zukata ga iyalai da al'ummar da suka yi rashin 'yan uwansu. Ya bayyana cewa kasancewarsa tare da jama'a a irin wannan lokaci na nuna kishin al'umma da kuma nagartaccen shugabanci.
"Zuwanka ya kwantar mana da hankali, ya ƙarfafa mana gwiwa, kuma ya tabbatar mana da cewa kana tare da al'ummarka a lokutan farin ciki da na baƙin ciki. Wannan ɗabi'a ta ƙwarai alama ce ta shugabanci na gari da kulawa da rayuwar jama'a."
Ya kuma yi addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka masa da mafificin alheri, Ya ƙara masa lafiya, hikima, ɗaukaka da nasara a dukkan al'amuransa.
Haka kuma, ya roƙi Allah Ya jikansa mamatan da rahama, Ya gafarta musu kurakuransu, Ya sanya Aljannar Firdausi ta zama makomarsu, tare da bai wa iyalai da daukacin al'umma haƙurin jure wannan babban rashi.
— Insight Tribune News



Comments
Post a Comment