HON. MUHAMMAD NAZIRU JAHUN YA ƘARA ƘARFAFA TAWAGAR YAƊA LABARAI DA TALLAFIN DATA DA KATIN WAYA
SPONSORED
Daga Hussaini Muhammad Tsakuwawa
A wani yunkuri na ƙara ƙarfafa harkokin sadarwa da yaɗa bayanai, ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai neman wakiltar Miga/Jahun Federal Constituency, Hon. Muhammad Naziru Jahun (Dan Gadawa), ya rabawa mambobin tawagar yaɗa labaransa katunan waya da data domin sauƙaƙa musu gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Wannan tallafi na zuwa ne a daidai lokacin da kafafen sadarwa da kafofin sada zumunta ke taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan al'umma da kuma isar da sahihan bayanai cikin gaggawa. Matakin ya nuna yadda Hon. Muhammad Naziru Jahun ke fahimtar muhimmancin sadarwa a matsayin ginshiƙin haɗin kai da ci gaba.
Masu anfani da tallafin sun bayyana jin daɗinsu tare da yabawa wannan mataki, suna mai cewa hakan zai ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da isar da saƙonnin alheri, ayyukan ci gaba, da manufofin jagorancinsa ga al'ummar mazabar Miga da Jahun.
Masu lura da al'amuran siyasa sun bayyana wannan mataki a matsayin wata alama ta jagoranci mai hangen nesa, inda shugaba ke nuna kulawa ga waɗanda ke aiki tare da shi wajen gina kyakkyawar alaƙa tsakanin al'umma da shugabanci.
Lallai, Hon. Muhammad Naziru Jahun na ci gaba da nuna cewa jagoranci na gari ba wai magana kaɗai ba ce, illa aiki, kulawa da kuma ƙarfafa gwiwar jama'a domin samun ci gaba mai ɗorewa.
Insight Tribune News

Comments
Post a Comment