GASKIYA ƊAYA CE


 

By Umar Umb Bauchi

Gaskiya ba ta da fuska biyu. Ko da an yi ƙoƙarin ɓoye ta, lokaci kan zo da take bayyana fili. Mutanen kirki sukan fuskanci ƙalubale, amma gaskiya tana da hanyar da take kare masu ita.

Dr. Bala Maijama’a Wunti ya kasance mutum mai sadaukarwa ga ci gaban al’umma, inda ayyukansa na alheri da taimakon jama'a suka zama abin shaida ga nagarta da kishin talaka. Abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda ya zaɓi aiki maimakon surutu, yana barin ayyukansa su yi magana a madadinsa.

A yau, saƙon da ya kamata mu fahimta shi ne cewa gaskiya ɗaya ce. Ba ta canzawa saboda ra’ayi ko zato. Duk wanda yake tafiya a kan tafarkin gaskiya, ko da ya ɗan fuskanci ƙalubale, ƙarshen al’amari nasara ce da ɗaukaka.

Allah Ya ci gaba da kare masu gaskiya, Ya ƙara wa Dr. Bala Maijama’a Wunti lafiya, albarka da nasara a dukkan al’amuransa.

Insight Tribune News

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

Prof. Hadiza Abdullahi Usman Celebrates Prof. Ahmed Ahidjo on Inaugural Lecture and Send-Forth

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS