DAN MALIKIN PALI, ALH. DANJUMA INUWA AIB, YA YABAWA AL’UMMA TARE DA KIRA GA HADIN KAI DA ZAMAN LAFIYA
Dan takarar kujerar Majalisar Jihar Bauchi mai wakiltar Alkaleri LGA/Pali Constituency karkashin jam’iyyar APM, Alh. Danjuma Inuwa AIB (Dan Malikin Pali), ya bayyana jin dadinsa da godiyarsa ga al’ummar mazabar bisa irin goyon baya, addu’o’i da gudunmawar da suke ci gaba da ba shi.
Alh. Danjuma Inuwa ya ce karfin guiwa da amincewar da jama’a suka nuna masa ne ke kara masa himma wajen ci gaba da sadaukar da kansa domin ci gaban al’umma da bunkasar yankin Pali Constituency.
Ya kuma yi kira ga daukacin al’umma da su ci gaba da tabbatar da hadin kai, zaman lafiya da mutunta juna, yana mai jaddada cewa ci gaban kowace al’umma na samuwa ne idan aka rungumi zaman lafiya da fahimtar juna.
Dan Malikin Pali ya bukaci matasa, mata da dattawa da su kasance masu bin doka da oda tare da gudanar da dukkan shirye-shiryen siyasa cikin lumana da mutunta ra’ayoyin juna. Ya ce siyasa hanya ce ta kawo ci gaba, ba ta rikici ko rarrabuwar kawuna ba.
A karshe, ya sake mika godiyarsa ga al’ummar Alkaleri LGA da Pali Constituency, yana mai tabbatar musu da cewa zai ci gaba da kasancewa tare da su a kowane lokaci domin kare muradunsu da tallafa wa duk wani yunkuri na ci gaba da ci gaban yankin.
Insight Tribune News

Comments
Post a Comment