DAMBAM EMIRATE COUNCIL TA YABA DA GOYON BAYA A NADIN JAGABAN MISAU
Masarautar Dambam karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Dambam, Alhaji Idris Bappa Musa, ta fitar da takardar godiya ga manyan baki da suka halarci bikin nadin Dr. Ahmad Umar Abdullahi, Wazirin Dambam, da sarautar Jagaban Misau.
A cikin takardar godiyar mai dauke da kwanan wata 14 ga Yuli, 2026, Majalisar Masarautar Dambam ta bayyana cewa halartar taron da dimbin jama'a da manyan baki suka yi ya kara wa bikin armashi, daraja da kuma nuna kyakkyawar alaka tsakanin masarautu da fitattun mutane a al'umma.
Masarautar ta jaddada cewa goyon baya, hadin kai da lokutan da mahalarta suka sadaukar wajen taya su murnar wannan gagarumin ci gaba abin yabo ne, kuma yana nuna kishin al'adu da martabar cibiyoyin gargajiya.
Hakazalika, Masarautar Dambam ta yi addu'ar Allah SWT Ya ci gaba da albarkaci duk wadanda suka halarci taron da lafiya, hikima da nasarori a rayuwarsu.
Takardar godiyar ta samu sanya hannun Dr. Ahmad Umar Abdullahi (Wazirin Dambam/Jagaban Misau), Babban Kansila na Masarautar Dambam.
– Insight Tribune News

Comments
Post a Comment