BATUN CEWA DR. BALA MAIJAMA’A WUNTI YA YADANI BA GASKIYA BA CE – ALH. UMAR UMB BAUCHI
KOMAI LOKACI NE – ALH. UMAR UMB BAUCHI
Daga: Insight Tribune News
Alh. Umar Umb Bauchi ya bayyana cewa dangantakarsa da Dr. Bala Maijama’a Wunti tana nan daram kamar yadda aka saba, yana mai cewa babu wani saɓani ko rashin fahimta a tsakaninsu.
A cewarsa, Dr. Bala Wunti mutum ne da yake da tarin ayyuka da nauyin hidimar al’umma, don haka akwai lokutan da yanayi da ayyuka kan rage yawan mu’amala tsakanin mutane ba tare da hakan ya sauya kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsu ba.
“Dr. Bala Maijama’a Wunti ubana ne, jagora ne kuma mutum ne da nake matuƙar girmamawa. Babu wata matsala a tsakaninmu. Na san nauyin da yake ɗauke da shi na hidimar jama’a, kuma ina ci gaba da yi masa fatan alheri da nasara a dukkan ayyukansa,” in ji Umar Umb Bauchi.
Ya ƙara da cewa ƙofofinsa a buɗe suke domin ci gaba da hidima tare da bayar da gudunmawa ga duk wani aiki na alheri da ci gaban al’umma da Dr. Bala Wunti ke jagoranta.
“Ni a gare ni, wannan dangantaka ta ginu ne a kan girmamawa, amana da kyakkyawar niyya. Ina fatan Allah Ya ci gaba da ba mu damar yin aiki tare wajen yi wa al’umma hidima kamar yadda muka saba.”
Alh. Umar Umb Bauchi ya kuma yi addu’ar Allah Ya ƙara wa Dr. Bala Maijama’a Wunti lafiya, albarka da nasara, tare da fatan ci gaba da samun damar amfana da shawarwari da jagorancinsa a nan gaba.

Comments
Post a Comment