Alh. Umar Umb Ya Yabawa Dr. Adamu Abdullahi Atterwahmie Kan Ayyukan Ci Gaba da Hidimtawa Al’umma
Alh. Umar Umb ya bayyana matuƙar jin daɗinsa tare da yabawa Mai Girma Medical Director na Federal Medical Centre (FMC) Birnin Kudu, Dr. Adamu Abdullahi Atterwahmie, bisa irin jajircewa, hangen nesa da shugabanci nagari da yake nunawa wajen bunƙasa harkokin lafiya da walwalar al’umma.
Ya musamman yaba masa kan samar da guraben ayyukan yi ga al’umma, musamman matasa, wanda hakan ya taimaka wajen rage zaman kashe wando tare da buɗe ƙofofin samun ci gaba da dogaro da kai ga dimbin matasa.
Haka kuma, ya jinjina masa kan gagarumin ci gaban da ake samu a Federal Medical Centre Birnin Kudu, inda asibitin ke ci gaba da samun sauye-sauye masu amfani ta fuskar kayan aiki na zamani, inganta ayyukan ma’aikata da kuma kyautata kula da marasa lafiya.
A cewarsa, Dr. Atterwahmie ya kasance shugaba mai hangen nesa wanda ke amfani da ilimi, ƙwarewa da fasahar zamani wajen kawo ci gaba mai ɗorewa, tare da sauya rayuwar al’umma ta hanyar ayyukan da suka shafi lafiya, ci gaba da walwala.
Alh. Umar Umb ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara wa Dr. Adamu Abdullahi Atterwahmie lafiya, hikima da nasara, Ya buɗe masa ƙofofin alheri da babban rabo, Ya ƙara albarka ga Jihar Jigawa, sannan Ya ba shi ikon ci gaba da yi wa jihar da al’ummarta hidima cikin gaskiya, riƙon amana da kishin ci gaba.
Ya ƙara da cewa shugabanni irin Dr. Adamu Abdullahi Atterwahmie abin alfahari ne ga al’umma, domin suna amfani da mukamansu wajen kawo sauyi mai amfani, haɓaka ci gaban zamani da kuma kyautata rayuwar jama’a.

Comments
Post a Comment