Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo Ya Yi Kira Ga ’Yan Najeriya Kan Muhimmancin Lokaci da Rayuwa
Tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya jawo hankalin al’umma bayan wata wasiƙa mai cike da darussa da tunatarwa kan hakikanin rayuwa ta karade kafafen sada zumunta.
A cikin wasiƙar, Obasanjo ya bayyana cewa duk da cewa mutane da dama suna ganin rayuwa tana da tsawo, gaskiyar al’amari ita ce rayuwa tana wucewa cikin sauri fiye da yadda ake zato. Ya bayyana cewa yana da shekaru 94 a duniya, kuma hakan ya sa ya fahimci cewa lokaci na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar ɗan Adam.
Tsohon shugaban ƙasar ya yi nuni da yadda mutane da yawa ke ɓata shekaru suna jiran wani mataki na gaba kafin su more rayuwa. Ya bayyana cewa tun daga lokacin makaranta, aikin soja, aure, tarbiyyar yara har zuwa ritaya, rayuwarsa ta kasance cike da jiran wani lokaci na musamman da yake ganin zai kawo farin ciki.
Sai dai ya bayyana cewa a ƙarshe ya fahimci cewa rayuwa ba ta tsaya jiran kowa ba, kuma farin ciki ba ya cikin jiran gobe, sai dai a cikin yadda mutum yake amfani da yau.
Obasanjo ya kuma yi magana kan dukiya, mulki da shahara, yana mai cewa duk waɗannan abubuwa ba su dawwama. Ya jaddada cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne kyawawan ayyuka, gaskiya, amana, taimakon jama'a da kuma irin kyakkyawan tarihin da mutum zai bari a bayansa.
Wasiƙar ta zama wata muhimmiyar tunatarwa ga ’yan Najeriya musamman matasa, kan muhimmancin amfani da lokaci yadda ya kamata, gina kyawawan halaye, da rayuwa mai anfani ga al’umma.
“Rayuwa gajera ce fiye da yadda muke zato. Kada ku rayu cikin jiran gobe; ku yi amfani da yau wajen aikata alheri da gina makoma mai kyau.”
— Insight Tribune News

Comments
Post a Comment