TSOHON MAI MAGANA DA YAWUN RUNDUNAR SOJIN NIGERIYA, MANJO JANAR ABUBAKAR RABE, YA RASU A HANNUN ƳANBINDIGA

 

TSOHON MAI MAGANA DA YAWUN RUNDUNAR SOJIN NIGERIYA, MANJO JANAR ABUBAKAR RABE, YA RASU A HANNUN ƳANBINDIGA


Insight Tribune News | Umar Umb Bauchi ✍️


An shiga jimami bayan rasuwar tsohon mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Abubakar Rabe (mai ritaya), wanda ya rasu yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Katsina.


Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya rasu ne a ranar Asabar, 13 ga Yunin 2026, bayan shafe wani lokaci a hannun ƴanbindiga da suka yi garkuwa da shi.


Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da rasuwar tasa ta bakin Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, Alhaji Nasiru Mu’azu, wanda ya bayyana cewa marigayin ya rasu ne sakamakon ta'azzarar cutar siga da hawan jini yayin da yake cikin halin tsarewa.


Sanarwar ta ce gwamnatin jihar tare da jami’an tsaro sun yi iya ƙoƙarinsu wajen ganin an kuɓutar da shi cikin ƙoshin lafiya, amma abin takaici ba a samu nasarar ceto shi da rai ba.


Marigayi Manjo Janar Abubakar Rabe ya kasance fitaccen jami’in soja wanda ya yi wa Najeriya hidima a fannoni daban-daban, ciki har da kasancewa mai magana da yawun rundunar sojin ƙasar. An san shi da kwarewa, jajircewa da sadaukar da kai wajen kare martaba da tsaron ƙasa.


Rasuwar tasa ta haifar da alhini a tsakanin iyalansa, abokan aikinsa, al'ummar Jihar Katsina da ma Najeriya baki ɗaya, inda mutane da dama ke ci gaba da miƙa ta'aziyyarsu tare da addu'ar Allah Ya jikansa da rahama.


Muna addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, Ya kuma bai wa iyalansa, abokansa da ƙasa baki ɗaya haƙurin jure wannan babban rashi. Amin.


Insight Tribune News

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

Prof. Hadiza Abdullahi Usman Celebrates Prof. Ahmed Ahidjo on Inaugural Lecture and Send-Forth

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS