TARIHIN NAGARTA DA KYAKKYAWAR JAGORANCIN DR. ADAMU ABDULLAHI ATTERWAHMIE
TARIHIN NAGARTA DA KYAKKYAWAR JAGORANCIN DR. ADAMU ABDULLAHI ATTERWAHMIE
Dr. Adamu Abdullahi Atterwahmie fitaccen likita ne kuma ƙwararren masani a fannin mata da haihuwa (Consultant Obstetrician and Gynaecologist), wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ceto rayuka da inganta harkokin kiwon lafiya a Najeriya. A halin yanzu shi ne Medical Director na Federal Medical Centre Birnin Kudu, inda yake jagorantar manyan sauye-sauye da ci gaba a cibiyar lafiya.
An haifi Dr. Atterwahmie a garin Atawame da ke ƙaramar hukumar Jahun a Jihar Jigawa. Ya yi karatun likitanci (MBBS) a University of Maiduguri, sannan ya ƙware a fannin mata da haihuwa bayan kammala horonsa na ƙwarewa. Kafin zamansa Medical Director na FMC Birnin Kudu, ya yi aiki a FMC Nguru inda ya riƙe muƙamai daban-daban ciki har da Shugaban Sashen Obstetrics and Gynaecology da kuma Mataimakin Shugaban Harkokin Kiwon Lafiya da Horaswa.
Tun bayan hawansa shugabancin FMC Birnin Kudu a shekarar 2021, ya kawo gagarumin ci gaba ta fuskar gine-gine, kayan aiki na zamani, ƙara yawan ma'aikata da bunƙasa ayyukan jinya. A ƙarƙashin jagorancinsa an faɗaɗa ayyukan asibitin, an samar da sabbin cibiyoyin kula da lafiya, tare da ƙaddamar da manyan ayyukan raya asibitin domin biyan buƙatun al'umma.
Dr. Atterwahmie mutum ne mai tausayi da kishin al'umma, wanda ya shahara wajen tallafawa shirye-shiryen lafiyar mata da yara, horas da matasa likitoci, da kuma jagorantar shirye-shiryen kiwon lafiya a matakin ƙasa da jihohi. Haka kuma shi Babban Mai Jarrabawa ne a West African College of Surgeons, alamar ƙwarewarsa da amincewar da masana suka yi masa.
Nagartarsa ta sa ya samu yabo daga gwamnati, sarakuna, ma'aikatan lafiya da al'umma baki ɗaya, saboda gaskiya, ƙwazo, jajircewa da hangen nesa wajen inganta rayuwar jama'a. A yau, Dr. Adamu Abdullahi Atterwahmie na daga cikin fitattun shugabannin kiwon lafiya da suka kafa tarihi a Arewacin Najeriya.
Alh. Umar Umb ✍️
Publisher/Editor-in-Chief, Insight Tribune News

Comments
Post a Comment