TAFIYAR AJIYA TA ƘARA ƊAUKAR SAITI A ƘARAMAR HUKUMAR ILLELA

 


TAFIYAR AJIYA TA ƘARA ƊAUKAR SAITI A ƘARAMAR HUKUMAR ILLELA


Tafiyar neman goyon bayan Alh. Umar Ajiya Isa (Ajiyan Sokoto), ɗan takarar kujerar Sanatan Sakkwato ta Gabas, na ci gaba da samun karɓuwa da goyon baya daga al'ummomi da masu ruwa da tsaki a sassa daban-daban na yankin.


A wani sabon mataki na ƙara bunƙasa yaƙin neman zaɓen, Campaign Coordinator na Ajiyan Sokoto a Ƙaramar Hukumar Illela, Alh. Kabiru Mado Amarawa (Garkuwan Illela), ya ɗauki nauyin sanya manyan allunan talla (billboards) a muhimman wurare domin ƙara wayar da kan jama'a da kuma nuna goyon bayansa ga ɗan takarar.


An girke allunan ne a wurare masu muhimmanci da suka haɗa da hanyar shiga garuruwan Illela da Amarawa, tare da bakin sakatariyar Ƙaramar Hukumar Illela, inda dubban mutane ke wucewa a kullum.


Masu sa ido kan harkokin siyasa a yankin sun bayyana wannan mataki a matsayin wata alama da ke nuna yadda tafiyar Ajiyan Sokoto ke ƙara samun karɓuwa da goyon baya daga al'ummar Sakkwato ta Gabas, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027.


Al'ummar yankin sun yabawa Alh. Kabiru Mado Amarawa bisa jajircewarsa da sadaukar da kai wajen tabbatar da nasarar tafiyar Ajiyan Sokoto, tare da bayyana cewa irin wannan gudunmawa na taimakawa wajen isar da saƙon sauyi da ci gaba ga jama'a.


Aiki yana tafiya yadda ya kamata, kuma tafiyar Ajiyan Sokoto na ci gaba da ɗaukar sabon salo da ƙarfi a sassa daban-daban na Sakkwato ta Gabas.


✍️ Umar Umb

Publisher, Insight Tribune News

Comments

Popular posts from this blog

The Woman Behind Clinical Excellence at FMC Birnin Kudu

Prof. Hadiza Abdullahi Usman Celebrates Prof. Ahmed Ahidjo on Inaugural Lecture and Send-Forth

FEC APPROVES FOUR KEY HEALTH INTERVENTIONS TO IMPROVE THE WELL-BEING OF NIGERIANS