SHIRU TAFI MAGANA ƘARFI A LOKUTA DA DAMA: DR. BALA MAIJAMA’A WUNTI ZAI SAMU TIKITI KUMA YA ZAMO ƊAN TAKARAR GWAMNAN JIHAR BAUCHI A APC 2027 – UMAR UMB
A siyasar Bauchi ta yau, ana ci gaba da jin ra'ayoyi daban-daban daga mabambantan ɓangarori dangane da zaɓen shekarar 2027. Duk da haka, a wasu lokutan shiru kan fi kowace magana ƙarfi wajen bayyana gaskiya da kuma nuna ƙarfin mutum a idon jama'a.
Dr. Bala Maijama’a Wunti ya kasance mutum mai hangen nesa, ƙwarewa, da kuma tarihin ayyukan alheri da suka shafi rayuwar al’umma. Duk da cewa bai cika shiga hayaniyar siyasa ko yin surutun neman suna ba, amma ayyukansa da gudummawar da yake bayarwa ga jama'a suna ci gaba da magana a madadinsa.
A cewar Umar Umb, lokaci zai tabbatar da cewa Dr. Bala Maijama’a Wunti yana daga cikin mutanen da suka cancanci jagorantar Jihar Bauchi zuwa wani sabon mataki na ci gaba. Ya bayyana cewa yawan goyon bayan da Dr. Wunti ke samu daga matasa, dattawa, mata, da sauran al’umma na ƙara ƙarfafa fata cewa zai samu tikitin Jam’iyyar APC kuma ya zama ɗan takarar gwamnan jihar Bauchi a zaɓen shekarar 2027, Insha’Allah.
"Shiru tafi magana ƙarfi a lokuta da dama. Yayin da wasu ke ta surutu, wasu kuma suna ci gaba da gina amana da soyayya a zukatan jama'a. Dr. Bala Maijama’a Wunti na daga cikin irin waɗannan mutane da ayyukansu ke magana a madadinsu," inji Umar Umb.
Ya ƙara da cewa tarihin Dr. Wunti na taimakon al’umma, bunƙasa ilimi, tallafawa matasa, da kuma ƙoƙarin inganta rayuwar jama'a ya sanya mutane da dama ke kallonsa a matsayin jagoran da zai iya kawo sauyi mai ma'ana a Jihar Bauchi.
Umar Umb ya yi addu'ar Allah Ya ba Dr. Bala Maijama’a Wunti nasara a dukkan al'amuransa, Ya kuma sanya alheri da ci gaba ga Jihar Bauchi da al'ummarta baki ɗaya.
– Insight Tribune News

Comments
Post a Comment