Shekaru Uku na Gwamna Ahmed Aliyu: Gina Tubalan Cigaba, Fuskantar Kalubale, da Hanyar Gaba ga Jihar Sakkwato
Daga
NASIRU YAHAYA ISA, M.Sc, MDS, MBA, FMLSCN, FAMLSN, FCIM, FIICA
Shekaru uku a kan mulki lokaci ne da ya isa a daina kallon gwamnati da idon alkawuran yaƙin neman zaɓe, a fara tantance ta bisa ayyukan da ta aiwatar. A irin wannan lokaci ne manufofi, tsare-tsare da salon shugabanci ke bayyana tasirinsu a rayuwar al’umma.
Yayin da Gwamna Ahmed Aliyu ke cika shekaru uku a mulki, Jihar Sakkwato na cikin wani muhimmin mataki da ya dace a yi nazari kan nasarorin gwamnatin, a tantance kalubalen da har yanzu ke gabanta, tare da gano damar da za su taimaka wajen gina makoma mai kyau.
Lokacin da Gwamna Ahmed Aliyu ya hau mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, jama’a sun ɗora masa manyan tsammanin nasara. Jihar ta fito ne daga zaɓe mai zafi, yayin da al’ummomi da dama musamman a yankin Sanatan Gabashin Sakkwato ke fama da matsalar tsaro.
A wancan lokaci, hanyoyi da sauran muhimman kayayyakin more rayuwa sun buƙaci gyara cikin gaggawa, amincewar jama’a ga gwamnati na buƙatar dawo da ita, kuma al’umma suna sa ran gwamnatin da za ta dawo da bege ta hanyar ayyukan ci gaba masu anfani ga talakawa.
Bayan shekaru uku, gwamnatin ta nuna ƙoƙari sosai wajen inganta ababen more rayuwa, ilimi, lafiya, walwalar jama’a da kuma kafa tubalan bunƙasar tattalin arziki. Sai dai kuma kamar yadda yake a sauran jihohin Arewa maso Yamma, har yanzu matsalar tsaro tana ci gaba da zama babban ƙalubalen da ke barazana ga waɗannan nasarori.
Tun daga farko, gwamnatin Ahmed Aliyu ta mayar da hankali kan gyaran hanyoyi, ilimi, lafiya, noma, samar da ruwa, ƙarfafa matasa, tsaro, bunƙasa tattalin arziki da walwalar jama’a. Duk da bambancin ra’ayoyi kan saurin aiwatar da ayyuka, babu shakka ci gaba ya fi bayyana a sassa daban-daban na jihar.
Ayyukan More Rayuwa
Daya daga cikin manyan nasarorin gwamnatin shi ne gyaran hanyoyi. A cikin birnin Sakkwato, an sake gina manyan hanyoyi uku a yankin Mabera wanda ya dade yana fama da ambaliyar ruwa. Hakan ya taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirga tare da rage matsalar ambaliya.
Haka kuma ana ci gaba da ayyukan hanyoyi a karkara kamar hanyar Illela zuwa Gada, tare da ayyukan gidaje a Wajake, Gidan Salanke da Sabon Garin Sakkwato.
Ilimi
A bangaren ilimi, gwamnati ta gyara tare da gina makarantu a dukkan ƙananan hukumomi 23 na jihar ta hannun SUBEB da shirin AGILE.
Makarantu a Wamakko, Bodinga, Tambuwal, Gwadabawa, Goronyo da Sokoto North sun amfana da sabbin ajujuwa, kayan zama, dakunan gwaje-gwaje da wuraren tsafta. Haka kuma ana ci gaba da inganta manyan makarantu tare da kula da walwalar malamai.
Lafiya
Bangaren lafiya ya samu kulawa sosai. An gyara asibitoci tare da samar da sabbin kayan aikin lafiya na zamani. Haka kuma an gyara cibiyoyin lafiya na matakin farko a sassa daban-daban na jihar.
Samar da Ruwa
Gwamnatin ta fara gyaran manyan cibiyoyin samar da ruwa ciki har da Sokoto Township Water Works, tare da gyaran cibiyoyin ruwa na Tamaje, Mana da sauran yankuna domin rage matsalar ƙarancin ruwa.
Noma
Da yake noma shi ne ginshikin tattalin arzikin jihar, gwamnati ta raba takin zamani, iri masu inganci, magungunan kashe kwari da kayan aikin noma ga manoma.
An kuma gyara madatsun ruwa na Lugu da Kware domin bunƙasa noman rani tare da samar da sababbin taraktoci domin ƙarfafa aikin noma.
Walwalar Jama’a
Gwamnatin ta biya basussukan fansho da kuɗaɗen gratuti ga ma’aikatan da suka yi ritaya, lamarin da ya rage musu wahalhalu.
Ta hannun shirye-shiryen NG-CARES da Ahmadu-CARES, dubban mata, matasa da ‘yan kasuwa sun samu tallafin kuɗi da hanyoyin dogaro da kai.
Harkokin Addini
Gwamna Ahmed Aliyu ya gina tare da gyara masallatan Juma’a da dama a cikin da wajen birnin Sakkwato. Haka kuma yana bayar da kuɗaɗen kula da masallatai duk wata, tare da horas da limamai da ladanai domin inganta ayyukan addini.
Tallafawa Wadanda Matsalar Tsaro Ta Shafa
Gwamnatin ta tallafawa al’ummomin da matsalar tsaro ta shafa musamman a Isa, Sabon Birni, Rabah da Wurno.
An kammala gidaje 100 ga ‘yan gudun hijira a Illela tare da kafa harsashin wani sabon aikin gidaje a Rabah.
Babban Kalubale: Tsaro
Duk da wadannan nasarori, matsalar tsaro na ci gaba da zama babban ƙalubale ga jihar.
Yankunan Isa, Sabon Birni, Goronyo, Rabah da wasu sassan Gwadabawa da Illela sun dade suna fama da hare-haren ‘yan bindiga wanda ya haddasa raba mutane da muhallansu, durƙusar da noma da rage ayyukan gwamnati.
Matsalar tsaro ta sa ayyukan ci gaba suka fi tsada, malamai da ma’aikatan lafiya suna gujewa zuwa wasu yankuna, yayin da masu zuba jari ke nuna shakku wajen saka hannun jari.
Gwamnatin jihar na ci gaba da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro na tarayya ta hanyar samar da tallafi da kayan aiki, amma har yanzu akwai buƙatar ƙarin matakai domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.
Damar Da Ke Gaba
Yayin da Gwamna Ahmed Aliyu ke shiga rabin ƙarshe na wa’adinsa na farko, akwai damar:
- Faɗaɗa ayyukan ci gaba a karkara.
- Ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu.
- Inganta lafiyar mata da yara.
- Bunƙasa masana’antun sarrafa kayayyakin noma.
- Amfani da gudunmawar shugabannin al’umma da masu hannu da shuni.
Gudunmawar Umar Ajiya Isa
Daya daga cikin mutanen da gudunmawarsu ta ja hankalin jama’a shi ne ɗan takarar Sanatan Gabashin Sakkwato na APC, Umar Ajiya Isa (Ajiyan Sakkwato).
Tsawon shekaru yana gudanar da ayyukan ci gaba musamman a bangaren lafiya, hanyoyi da tallafin jin ƙai.
Ya samar da hasken rana ga manyan asibitocin Isa, Sabon Birni, Goronyo, Rabah da Wurno. Haka kuma ya taimaka wajen samar da babban asibitin zamani da NNPCL ta gina a hanyar Filin Jirgin Sama na Sakkwato.
Ayyukansa sun haɗa da gina hanyar Isa zuwa Kwanar Isa mai tsawon kusan kilomita 10 da darajarta ta kai kusan naira biliyan ɗaya.
Bayan zama ɗan takarar Sanata, ya ci gaba da samar da hasken rana ga asibitocin Illela, Gwadabawa da Gada, tare da raba kayan haihuwa ga mata masu juna biyu.
Ya kuma tallafawa waɗanda hadurran mota, hare-haren ‘yan bindiga da bala’o’in iska suka shafa a yankuna daban-daban.
Shekaru uku ba su isa su kammala tarihin kowace gwamnati ba. Amma gwamnatin Ahmed Aliyu ta nuna ƙuduri wajen inganta more rayuwa, ilimi, lafiya da walwalar jama’a duk da matsalolin kuɗi da tsaro.
Sai dai nasarar ta gaba za ta dogara ne da yadda za a samu zaman lafiya mai ɗorewa, bunƙasa karkara da samar da damar tattalin arziki ga matasa.
An shimfiɗa tubalan ci gaba. Yanzu abin da ake buƙata shi ne ƙara sauri, faɗaɗa anfani ga kowa, da kuma ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro, ci gaba da kyakkyawan shugabanci.
Tarihi yakan tuna gwamnatoci ne ba kawai saboda ayyukan da suka yi ba, har ma saboda irin tasirin da suka bari a rayuwar al’umma. Ga Jihar Sakkwato, shekaru masu zuwa za su zama wata dama ta mayar da nasarorin yau zuwa ci gaba mai ɗorewa ga al’ummomin gobe.
Nasiru Yahaya Isa (Wamban Isa), tsohon Babban Sakataren Gwamnati ne, kuma Mai Kula da Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen Ajiyan Sakkwato na Majalisar Dattawa, ya rubuta wannan makala daga Sakkwato.

Comments
Post a Comment